Muhimman Abubuwa 7 Da Tinubu Ya Aiwatar a Cikin Kwanaki 7 Na Shekarar 2024, In Ji Onoh

Muhimman Abubuwa 7 Da Tinubu Ya Aiwatar a Cikin Kwanaki 7 Na Shekarar 2024, In Ji Onoh

  • A farkon shekarar 2024, Shugaba Tinubu ya aiwatar da wasu muhimman abubuwa da suka ba kowa mamaki a Najeriya
  • Tun daga sallamar ministar jin kai, Betta Edu, zuwa nada sabbin shugabannin hukumar alhazai ta Musulmi da Kirista
  • Dr. Josef Onoh ya zayyana wasu muhimman abubuwa bakwai da Tinubu ya yi a acikin kwanaki bakwai na shekarar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tsohon mai magana da yawun Shugaba Tinubu a lokacin yakin neman zabe daga shiyyar Kudu maso Gabas, Dr. Josef Onoh ya ce Tinubu ya taka rawar gani a cikin kwanaki 7 na sabuwar shekara.

Onoh ya yi nuni da cewa a cikin mako guda Tinubu ya nuna karfin ikon shugaban kasa da kuma yadda ya kamata shugaban ya kasance wajen daukar matakai.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da N-Power, Tinubu ya dauki matakin karshe kan shirin NSIPA, ya fadi dalili

Abubuwa 7 da Tinubu ya yi a farkon 2024
Manyan matakai 7 da Tinubu ya dauka a cikin kwanaki 7 da suka kara masa daraja. Hoto: @NGRPresident
Asali: Facebook

Onoh ya lissafa wasu muhimman abubuwa 7 da Tinubu ya yi a farkon shekarar 2024, kamar yadda The Guardian ta wallafo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DSS ta cafke mataimakiyar bankin CBN, Aisha Ahmed

Ya bayyana cewa matakin da Tinubu ya da dauka na ba hukumar tsaro ta DSS samar cafke mataimakiyar bankin CBN, Aisha Ahmed abin a yaba ne.

Ya ce DSS sun kama Ahmed ne kan zargin sa hannunta a mallakar bankunan Polaris, Titan, Union ba bisa ka'ida ba.

Shugaba Tinubu ya kori shugabannin bankunan Titan da wasu uku

Onoh ya bayyana cewa a kokarin Tinubu na tsaftace fannin kudi, ta hannun bankin CBN, shugaban ya ruguza shugabancin bankin Titan da wasu bankuna uku.

Kuma ya kara da cewa matakin korar dukkan shugabannin ya biyo bayan rahoton da mai bincike na musamman na CBN, Mr Jim Obazee ya gabatar masa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana babban abin da ya ke mutunta Tinubu da shi bayan hukuncin Kotun Koli

Tinubu ya dakatar da ministar jin kai, Dr. Betta Edu

A cewar Onoh:

"A farkon shekarar ne Shugaba Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ministar jin kai da kawar da fatara saboda zargin ta karkatar da wasu kudade.
"Hukumar EFCC ta binciki Edu jim kadan bayan dakatar da ita kan tura akalla naira miliyan 585 zuwa asusun wani jami'i da nufin karkatar da kudin."

Tinubu ya rage yawan kudade da mutane a tafiye-tafiyensa

Ya kara da cewa, Shugaba Tinubu a cewar mahukunta, ya rage yawan mutane da ke masa rakiya idan zai yi tafiya, kuma ya rage kudin da ake kashewa.

Ya ce hakan abu ne mai kyau wajen alkinta dukiyar al'umma musamman ma a tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare da na cikin gida, Leadership ta ruwaito.

Tinubu ya kori shugabannin hukumar FCCPC da BPE daga aiki

Jigon APC ya kuma ce matakin da Tinubu ya dauka na sallamar shugaban hukumar kare masu sayen kayayyaki ta kasa (FCCPC) da na hukumar kamfanoni (BPE) abin a yaba ne.

Kara karanta wannan

Hadiman Atiku 5 da su ka juya masa baya, suka yi aiki da Gwamnati da APC

A hannu daya kuma Tinubu ya nada sabbin shugabannin hukumar alhazai ta Musulmi (NAHCOM) da ta Kirista, da nufin bunkasa ayyukan hukumomin biyu.

Shugaba Tinubu ya sa ayi binciken 'digiri dan Kwatano'

A cewar Onoh:

"A kokarin sa cikin shekarar 2024, Tinubu ya ba da umurnin dakatar da amfani da kwalin digiri da aka samo daga wasu kasashen Afrika da suka hada da Togo, Benin da sauran su.
"Haka zalika Tinubu ya sanar da cewa gwamnatin sa za ta gina kamfanin tama da karafa a Abuja." (edited)

Tinubu ya biya Super Eagles bashin N12bn da suke bi

"Shugaba Tinubu ya ba da umurnin biyan bashin naira biliyan 12 ga kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da wasu kungiyoyin wasanni na kasar.
"Kuma Tinubu ya kawo zaman lafiya a kasar Sierra Leone bayan wani yunkuri na juyin mulki da ba a samu nasara ba."

A cewar Onoh.

Tinubu ya cancanci a jinjina masa - Murtala Sani

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

A zantawarsa da jaridar Legit Hausa, Murtala Sani, mazaunin garin Funtua da ke jihar Katsina ya ce lallai ya kamata 'yan Najeriya su yaba kokarin gwamnatin Shugaba Tinubu.

A cewar Sani, matakan da Shugaba Tinubu ke dauka kan cin hanci da rashawa shi ne kadai zai dawo da martabar aikin gwamnati a Najeriya, da kuma rage sace kudaden jama'a.

"Dama Hausawa sun ce sai an tauna tsakuwa aya take jin tsoro; yanzu duk wani mai rike da mukamin gwamnati zai shiga taitayinsa, ba zai bari a kama shi da laifin satar kudi ba.
"Abin da ya rage wa Shugaba Tinubu shi ne ya tabbatar da an hukunta duk wanda aka kama da laifin sata, hakan zai kara nuna gaskiyar sa a idon 'yan Najeriya"

A cewar Murtala Sani.

Matar Aure ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta

A wani labarin, wata matar aure Sa'adatu Ayuba, ta nemi kotu ta raba aurenta da mai gidanta Jalija saboda ba ya iya gamsar da ita a kwanciyar aure.

A yayin zaman kotun an gano cewa Sa'adatu da Jalija sun yi aure ne tun a shekarar 1997 kuma sun haifi yara biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.