Bayan Dakatar da N-Power, Tinubu Ya Dauki Matakin Karshe Kan Shirin NSIPA, Ya Fadi Dalili

Bayan Dakatar da N-Power, Tinubu Ya Dauki Matakin Karshe Kan Shirin NSIPA, Ya Fadi Dalili

  • Bayan dakatar da ayyukan N-Power da duk wata hukumar tallafa wa jama’a, Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti
  • Tinubu ya dauki matakin ne don tabbatar da bincike kan zargin badakalar da ta dabaibaye ma’aikatar jin kai
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Asabar 13 ga watan Janairu a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kafa kwamitin binciken shirin dogaro da kai da kuma N-Power a Najeriya.

Wannan mataki na Tinubu ya biy bayan zargin badakalar makudan kudade da aka samu a ma’aikatar jin kai da walwala.

Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai karfi kan shirin NSIPA
Tinubu ya dauki matakin ne don kwakkwaran bincike. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wane mataki Tinubu ya dauka?

Kara karanta wannan

Tinubu ya dakatar da shirin NSIPS da gwamnatin Buhari ta kirkira

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Asabar 13 ga watan Janairu a Abuja, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daukar matakin ya biyo bayan rushe shirin N-Power da Tinubu ya yi da kuma dakatar da Minsitar jin kai, Betta Edu.

Tinubu ya dakatar da shirin ne guda hudu da suke karkashin hukumar NSIPA har na tsawon makwanni shida.

Kwamitin da Tinubu ya kafa zai samu jagorancin Minsitan Kudade, Wale Edun da sauran mambobin kwamitin.

Wadanda ke cikin kwamitin

Sanarwar ta ce:

“Wannan kwamitin bincike na musamman an daura musu alhakin duba wa da kuma binciken kudade a hukumar tallafa wa jama’a.
“Don samar da daidaito da kuma sauya akalar kudaden hukumar da kuma inganta harkokin ma’aikatar da suka shafi al’umma.”

Har ila yau, kwamitin na dauke da Ministoci da ke wakiltar ma’aikatu daban-daban don daukar mataki da kawo sauyi, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Tinubu ya aiwatar a cikin kwanaki 7 na shekarar 2024, in ji Onoh

Mambobin kwamitin sun hada da:

1. Minsitan Tattalin Arziki da Kudade, Wale Edun – Shugaba

2. Ministan Lafiya da walwalar jama’a – Mamba

3. Minstan Kasafi da Tsare-tsare – Mamba

4. Minsitan Yada Labarai – Mamba

5. Ministan Sadarwa da Kirkire-kirkire – Mamba

6. Karamin Minsitan Matasa – Mamba

Tinubu ya soke shirin NSIPA

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da shirin NSIPA bayan samun badakala a ma’aikatar jin kai.

Daraktan labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen shi ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel