'Yan Ta’adda Sun Datsewa Masunta Hannu Kan Zargin Sata a Borno
Mayakan ISWAP sun yanke danyen hukunci kan wasu masunta guda biyu bayan da suka kama su kan zargin sun yi masu sata
Mai fashin baki kan harkon tsaro Zagazola Makama ne ya kawo labarin inda ya ce lamarin ya faru ne a garin Marte da ke jihar Borno
Rahotanni sun bayyana cewa masuntan na cikin wata babbar kungiyar masunta da ke karkashin ikon mayakan na ISWAP
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Borno - A baya-bayan nan ne mayakan ISWAP suka yanke hannun wasu masunta biyu a garin Marte da ke jihar Borno, bayan sun zarge su da satar kifi.
Masuntan sun kasance mambobin wata babbar kungiya da ke gudanar da ayyukan kamun kifi a karkashin ikon ISWAP, inda suke biyansu haraji da ihisani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai fashin baki kan harkokin tsaro, Zagaloza Makama ya wallafa hakan a safinsa na Twitter a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2023.
Abin da ya jawo makayan ISWAP suka datse hannun masunta
Zagaloza ya ruwaito cewa, masuntan biyu sun fuskanci fushin mayakan ne a lokacin da aka gano cewa ba su biya harajin su ba, sai ‘yan ta’addan suka tafi da kwandunan kifi guda takwas.
Bayan dora kifin a kan kwalekwalen nasu, rashin wadataccen wuri ya tilastawa mayakan jefar da da kwando guda biyu na kifin.
Ganin haka ya saka masuntan suka kwaso kwali biyu da aka yi watsi da su a asirce, wanda ya kai ga ISWAP ta kama su bisa zargin sun yi masu sata.
Bayan kamasu ne shugaban kungiyar ya bayar da umarnin a datse hannayen mutanen kamar yadda shari'a ta tanada.
Ga abin da ya rubuta:
Yan bindiga sun sace malamin jami'a a jihar Zamfara
A safiyar yau muka ruwaito maku cewa 'yan bindiga sun sace wani malamin jami'ar tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara bayan artabu da 'yan sanda da suka yi kokarin dakatar da su.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba inda 'yan bindigar suka shiga gidan malamin mai suna Bello Janbako suka yi awon gaba da shi, kamar yadda wani da abin ya faru a kan idon sa ya bayyana.
Asali: Legit.ng