Ku dauka mataki a kan masu sata, kada ku saurara musu - Buratai ga Kwamandojinsa

Ku dauka mataki a kan masu sata, kada ku saurara musu - Buratai ga Kwamandojinsa

- Sace-sace da asarori suna ta aukuwa a biranen jihohi da dama da sunan zanga-zangar EndSARS

- Shugaban rundunar soji, Tukur Buratai ya umarci sojoji da su dakatar da hakan

- Ya sanar da hakan ne a wani jawabi da yayi a taron da suka yi a hedkwatar tsaro da ke Abuja

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito yadda bata-gari suka yi ta amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin satar dukiyoyin al'umma, duk da kullen da aka yi ta sakawa a jihohin.

Sun cigaba da satar dukiyoyin gwamnati wadanda suka hada da kayan tallafin COVID-19, kayan shaguna, kasuwanni da sauran dukiyoyi.

Hatta ofisoshin 'yan sanda basu bar su ba, inda suka yi ta kone-kone.

Sifeta janar na 'yan sanda, ya umarci Jami'an 'yan sanda da su dakatar da duk wasu sace-sace a jihohi a ranar Asabar.

Ya umarci Jami'an da su tsaya a wuraren ofisoshin da aka kona don cigaba da bayar da tsaro.

Kwanaki 4 bayan an bayar da wannan umarnin ne bata-gari suka cigaba da sace-sacen a jihohi har da babban birnin tarayya, Abuja.

Yayin da Buratai ke gabatar da jawabi ga manyan kwamandojin a Hedkwatar tsaro dake Abuja, ya ce wajibi ne kwamandoji da jami'ansu su samar da zaman lafiya a kasa.

Ya kara da cewa, "Ba zan lamunci cin amanar gwamnati da almundahana ba daga wani jami'in tsaro, sakamakon sace-sace da asarorin da ake tafkawa a birane."

Bayan gama taron ne kakakin rundunar Sojin, Kanal Sagir Musa ya sanar da abubuwan da Buratai yayi jawabi a kai.

KU KARANTA: Yawan arzikin Obama da kuma hanyoyin da ya bi wurin mallakarsu

Ku dauka mataki a kan masu sata, kada ku saurara musu - Buratai ga Kwamandojinsa
Ku dauka mataki a kan masu sata, kada ku saurara musu - Buratai ga Kwamandojinsa. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Buratai ya bayyana abinda 'yan ta'adda ke shirya wa sojin Najeriya

A wani labari na daban, Bayan Jami'an tsaro sun fara bincike gidaje don nemo dukiyoyin gwamnati da na mutane wadanda aka sata, bata-gari sun fara yasar da kayan a bololi da kuma wasu wuraren buya a cikin garin.

Wannan lamarin ya faru ne bayan kwamishinan 'yan sanda, Abdulkadir Jimoh ya umarci duk wanda ya saci kayan da ya dawo da su cikin awanni 24, ko kuma ya fuskanci fushin hukuma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel