EFCC Ta Kama Shugaban Bankin Musulunci Na Ja’iz Kan Badakalar Betta Edu? Gaskiya Ta Bayyana
- Yayin da ake ci gaba da bincike kan badakalar dakatacciyar Ministar jin kai, Betta Edu, abin ya fara girma
- Ana tuhumar wasu bankuna da zargin karbar makudan kudade daga ma'aikatar jin kai ciki har da Ja'iz
- Sai dai bankin Musulunci na Ja'iz ya musanta cafke babban daraktan bankin kamar yadda ake yadawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar gudanarwa ta bankin Musulunci na Ja'iz ta yi martani kan zargin kama babban daraktan bankin.
Bankin ya karyata jita-jitar cewa hukumar EFCC ta cafke shugaban bankin kan badakalar Ministar jin kai, Betta Edu, cewar Tribune.
Mene ake zargin bankin Ja'iz?
Ya ce a jiya Talata 9 ga watan Janairu, sun mika wasu takardu ga hukumar EFCC kan wasu asusun bankuna da suka bude.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin Ja'iz ya ce sun mika takardun ne bayan hukumar EFCC ta bukaci hakan kan asusun bankuna da aka bude na ma'aikatar.
Har ila yau, bankin ya ce shugabansa ya gana da hukumar EFCC din cikin aminci kuma har ya dawo aiki kamar yadda aka saba.
Yayin da bankin ke karin bayani, ya tabbatar da cewa a watan Oktobar 2023 an zabi bankin daga cikin wadanda ma'aikatar za ta yi aiki da su.
Mene Ja'iz ke cewa kan zargin?
Hadin gwiwar an yi ta ne don tallafa wa marasa karfi wanda shi ne babban burin ma'aikatar tun farko.
Ja'iz ya kara da cewa an umarce shi ya bude asusun bankunan amma har yanzu ko sisin kwabo ba a tura cikin asusun bankunan ba.
Hukumar bankin ta ce ta himmatu wurin tabbatar da ba da gudunmawa don ci gaban Najeriya ta fannin tattalin arziki, cewar Daily Nigerian.
Bankin Ja'iz ya nada sabon shugaba
A wani labarin, Bankin Musulunci na Ja'iz ya amince da nadin sabon babban daraktan bankin don ci gaba da gudanar da bankin.
Bankin ya nada Haruna Musa a matsayin wanda zai jagoranci bankin bayan samun sahalewa daga Babban Bankin Najeriya, CBN.
Asali: Legit.ng