Bankin Musulunci, Jaiz, ta alanta samun ribar N2.4bn a shekarar 2019

Bankin Musulunci, Jaiz, ta alanta samun ribar N2.4bn a shekarar 2019

Shahrarren bankin da ke aikinta bisa koyarwan addinin Musulunci ta farko a Najeriya, Jaiz, ta sanar gagarumin ribar da ta samu bayan biyan harajin gwamnati a shekarar 2019.

Bankin ta samu ribar N2.4bn ba tare da ta'amuni da 'Riba' ba.

Dirakta manajan bankin, Hassan Usman, ya bayyana cewa bankin ta samu wannan nasara ne bisa namijin kokarin da ma'aikatan sukayi wajen gamsar da kwastamominsu.

Legit.ng Hausa ta samu wannan labari ne a jawabin da bakin ta saki a shafinta na Facebook da safiyar Juma'a, 5 ga watan Yuni, 2020.

KARANTA WANNAN: Za mu fara sallaman masu cutar Korona daga asibiti ko da basu warke ba - NCDC

Jawabin yace: "Jaiz Bank Plc, babbar banki maras ta'amuni da riba a Najeriya ta saki sakamakon aiki na shekara da ta kare 31 ga Disamba 2019, kuma ta alanta samun ribar N2.4bn bayan biyan haraji."

"A rahoton da bankin ta mikawa cibiyar lissafin jarin Najeriya NSE, bankin ta samu habakar riba kafin biyan haraji na shekara" daga N879.7m a 31 ga Disamban 2018.

"Abubuwan da akan iya tsamowa daga rahoton sune kudin shigar bankin ya girma da 80% zuwa N13.5bn a Disamban 2019, sabanin N7.5bn a bara."

"Hakazalika jimillar dukiyar bankin ta girma da 54% zuwa N167.27bn daga N108.46bn."

TAMBIHI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A bangare guda, Legit,ng ta kawo muku rahoton cewa Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa za ta sake shawara a kan matakin da ta cimma na bude wuraren ibada a kasar idan har ba a bin sharuddan da ta gindaya.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da korona na shugaban kasa, PTF, Boss Mustapha, a yayin jawabin kwamitin a ranar Alhamis ya ce an raba wa jihohi sharrudan.

Ya ce gwamnatin tarayya na sa ran shugabanin addinai za su amince da sharrudan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel