Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Babban Birnin Jihar Arewa Sun Tafka Ta'asa

Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Babban Birnin Jihar Arewa Sun Tafka Ta'asa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga har cikin birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara sun tafka aikin ta'addanci
  • Ƴan bindigan sun kutsa har cikin gidan wani darakta a ma'aikatar kuɗi ta jihar inda suka yi awon gaba da shi tare da matarsa da ƴaƴansa
  • Daga baya ƴan bindigan waɗanda alamu suka nuna kamar turo su aka yi sun sako matar saboda dalilin rashin lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani darakta a ma’aikatar kuɗi ta jihar Zamfara, Malam Sabiu da matarsa ​​da ƴaƴansa biyu.

Jaridar The Punch ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, a rukunin gidaje na Damba da ke Gusau, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan yan bindiga sun halaka babban basarake a gidansa

Yan bindiga sun sace darekta a Zamfara
Yan bindiga sun yi awon gaba da darekta a ma'aikatar kudi ta Zamfara Hoto: @Mfaarees
Asali: Twitter

Wani mazaunin yankin mai suna Auwalu Garba, ya ce ƴan bindigan sun shiga gidan Sabiu da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

A cewarsa, ƴan bindigan waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun je gidan Sabiu ne kai tsaye da isar su unguwar, wanda hakan ya nuna kamar umarni aka ba su.

A kalamansa:

"Lokacin da suka isa unguwarmu, ba su yi harbi ba, ba su kuma shiga gida ba. Kai tsaye gidan Sabiu suka nufa inda suka fasa ƙofar, suka shiga ɗakin barcinsa suka sace shi da matarsa.
"Daga baya suka koma wani ɗaki suka yi awon gaba da yara biyu sannan suka koma daji."

Garba ya ce daga baya ƴan bindiga sun sako matar Sabiu bisa dalilan rashin lafiya.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya ci tura, domin an kasa samunsa ta layin wayarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara binciken minista kan badakalar N585.2m

Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Rakyabu da ke ƙaramar hukumar tsafe ta jihar Zamfara.

A yayin farmakin dai da ƴan bindigan suka kai, sun yi awon gaba da Hakimin ƙauyen, Magaji Saodu tare da babban limamin ƙauyen Malam Abdullahi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng