Jerin Jami'o'in Najeriya Da Suka Yi Magana Kan Sunayen 'Farfesohin Boge' Da Ya Yadu

Jerin Jami'o'in Najeriya Da Suka Yi Magana Kan Sunayen 'Farfesohin Boge' Da Ya Yadu

Hukumar Kula da Jami'o'i na Kasa (NUC) ta yi watsi da rahoton da ke yawo na cewa an gano wasu farfesoshin bogi fiye da 100 wadanda ba a bayyana sunansu ba kuma aka danganta su da jami'o'in Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

A cewar Premium Times, Chris Maiyaki, mukadashin sakataren NUC, a hirar da aka yi da shi ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu, ya ce hukumar ba ta gano wani farfesan boge ba a halin yanzu.

Wasu jami'o'in Najeriya sunyi magana kan sunayen farfesoshin boge da aka fitar
Jami'o'in Najeriya da dama sun fito sun nesanta kansu daga jerin sunayen farfesohin bogi da aka fitar. Photo Credit: UNILORIN, UNILAG
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan daga bisani NUC ta fitar da sanarwar watsi da rahoton, da ya shafi jami'o'in tarayya da na jihohi.

UNILORIN

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

Jami'ar Ilorin ta musanta rahoton cewa tana da farfesoshin boge 11. Kunle Akogun, kakakin jami'ar, ya ce babu farfesoshin boge a jami'ar kuma ba su daukan farfesoshin boge aiki.

A cewar Akogun, dalilin yin karin hasken shine don tabbatarwa masu ruwa da tsaki cewa suna dade suna da tsatsauran tsarin bin dokoki da kiyayye ka'idoji.

Jami'ar Covenant

Jami'ar da ke jihar Ogun ita ma ta yi watsi da rahoton cewa tana da farfesohin boge.

Chichi Ononiwu, mai magana da yawun jami'ar, cikin sanarwa a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu, ya ce babu wani ma'aikacinsu cikin sunayen da ake yadawa.

Jami'ar Ibadan

Jami'ar Ibadan a jihar Oyo ita ma ta yi watsi da rahoton tana mai cewa ikirarin da aka yi na cewa akwai farfesoshin bogi a jami'ar ba shi da tushe.

Ganiyu Saliu, rajistara kuma sakataren majalisar jami'ar, cikin wata sanarwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ya ce sunayen da aka ambata a jerin sunayen da ke yawo a gari ba ma'aikatansu bane.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ya yi shagube ga Buhari

Jami'ar Babcock

Mahukunta a jami'ar mai zaman kanta a Ilisan Remo a jihar Ogun suma karyata cewa akwai farfesohin jami'arsu cikin sunayen da aka saki.

Direktan sadarwa da kasuwanci na jami'ar, Joshua Suleiman, ya yi tir da sunayen yana mai cewa makirci ne da masu neman tada tsaye suka shirya.

Jami'ar Redeemers

Jami'ar da ke jihar Osun ita ma ta karyata rahoton cewa tana da farfesoshi na boge, tana mai cewa babu wasu masu sunayen a cikin ma'aikatanta.

Adetunji Adeleye, mataimakin direkta na harkokin hukumomi na Jami'ar ta Redeemers ya ce sunayen da aka fitar da cewa farfesohin bogi ne ba su taba aiki a jami'ar ba.

Sauran jami'o'in da suka ce ba su da farfesoshin boge sune:

  1. Jami'ar Legas
  2. Jami'ar Fasaha ta Tarayya (FUTA)
  3. Jami'ar Bayero ta Kano (BUK)

Asali: Legit.ng

Online view pixel