Innalillahi: Shahararren Malamin Addinin Musulunci Ya Rasu Ya Na da Shekaru 80 a Duniya
- Allah ya karbi rayuwar babban limamin Ibadan, Sheikh Abdulfatai Muhali Alaga a yau Talata a jihar Oyo
- Marigayin wanda shi ne babban limamin birnin Ibadan ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.
- Gwamna Seyi Makinde ya nuna alhini kan rasuwar marigayin da aka fi sani da Alfa Agba na Ibadan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Oyo, Sheikh Abdulfatai Muhali Alaga ya rasu.
Marigayin wanda shi ne babban limamin birnin Ibadan ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.
Yaushe malamin Musuluncin ya rasu?
Alaga ya rasu ne a yau Talata 9 ga watan Janairu inda aka binne shi da yammacin yau Talata da misalin karfe 4:00 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Seyi Makinde ya nuna kaduwarshi kan rasuwar marigayin da aka fi sani da Alfa Agba na Ibadan, cewar Punch.
Ya tura sakon jaje ga iyalan babban limamin Ibadan da kuma al'ummar Musulmi da ke jihar baki daya, cewar National Insight News.
Makinde ya ce tabbas marigayin ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.
Gwamnan ya ce tabbas rashin malamin ya bar wani babban gibi wanda zai yi wahalar cike wa, News Now ta tattaro.
Mene Gwamna Makinde ke cewa kan marigayin?
Ya ce:
"Na samu labarin rasuwar Sheikh Abdulfatai Muhali Alaga da safiyar yau Talata.
"Ina mika sakon ta'aziya ga babban limamin Ibadan, Sheikh Abdulganiyu da Musulmi a jihar Oyo kan wannan babban rashi."
Gwamna Seyi ya kuma tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya yi addu'ar ubangiji ya masa rahama da hakurin jure wannan rashi.
Ambasada Anka ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, Fitaccen dan siyasa a jihar Zamfara, M. Z Anka ya riga mu gidan gaskiya a jihar Sokoto.
Anka wanda ya kasance fitaccen dan siyasa ya rasu ne a jihar Sokoto bayan fama da jinya na tsawon lokaci.
Marigayin shi ne mahaifin kwamishinar harkokin kiwon lafiya a jihar Zamfara, Dakta Aisha M. Z Anka.
Asali: Legit.ng