A Karshe, an Cafke Sojan da Ya Yi Wa Gwamnan APC Rashin Kunya, Bayanai Sun Fito

A Karshe, an Cafke Sojan da Ya Yi Wa Gwamnan APC Rashin Kunya, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar cafke sojan da ya caccaki Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas
  • Hafsan sojin kasar, Taoreed Lagbaja shi ya tabbatar da haka inda ya ce sojan ya saba ka'idar aikin soja
  • A cikin wani faifan bidiyo, sojan ya caccaki gwamnan kan wani mataki da ya dauka kan wani soja da ya saba dokar hanya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Hafsan sojin Najeriya, Taoreed Lagbaja ta tabbatar da cewa sun kama sojan da ya caccaki Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas.

A cikin wani faifan bidiyo, sojan ya caccaki gwamnan kan wani mataki da ya dauka kan wani soja da ya saba dokar hanya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

"Burin kowane ɗan Najeriya ya ɗauki hoto da ni" Ministan Tinubu ya yi magana mai jan hankali

Sojoji sun kame sojan da ya yi rashin kunya ga Gwamnan APC
Sojoji sun kama sojan da ya caccaki Gwamna Sanwo-Olu. Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Nigerian Army.
Asali: Twitter

Mene rundunar ke cewa kan sojan?

Lagbaja ya ce tabbas sojan da aka kama ya saba dokar hanyar kuma ya karya ka'idojin da ake musu horo a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sauran faya-fayen bidiyon da aka nuno sojojin na kushe matakin gwamnan akwai na bogi, cewar The Nation.

Taoreed ya ce bidiyon guda daya da aka samu shi ne aka yi bincike har ya kai ga kama sojan, kamar yadda Punch ta tattaro.

Mene dalilin kama sojan a Legas?

Ya kara da cewa rundunar ta dauki matakai don nusar da sojoji yadda za su yi mu'amala a wurare da yawa a cikin al'umma.

Idan ba a manta ba, Gwamna Sanwo-Olu a ranar Talata 2 ga watan Janairu ya umarci kame wani jami'in soja bayan ya saba dokar hanya yayin tuki.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Legas zuwa Badagry inda aka kama sojan da wasu masu kabu-kabu saboda rashin bin ka'idar hanya.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne yayin da ya ke dawo wa daga wani babban taro a Jami'ar jihar Legas.

An yi cece-kuce bayan ganin gwamna a masallaci

A wani labarin, 'Yan Najeriya da damma sun yi ta cece-kuce bayan ganin Gwamna Sanwo-Olu a cikin masallaci.

Shugaba Tinubu ne ya shiga da gwamnan wanda Kirista ne cikin masallacin Juma'a a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.