Mutane 5 Wadanda Suka Fi Karfin Fada-Aji a Gwamnatin Buhari da Yanzu Aka Daina Jin Duriyarsu
- Abubuwa da dama sun faru a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, an sha dirama
- A gwamnatin sa ne aka yi ikirarin akwai wasu da ke juya akalar mulkin kasar da aka yi wa lakabi da 'cabal' a turance
- Sai dai tun bayan karewar wa'adin mulkin Buhari, aka nemi wadannan masu fada aji aka rasa, aka ma daina jin duriyar su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - A ranar 29 ga watan Mayu 2023, wa'adin mulkin Muhammadu Buhari na shekaru takwas ya zo karshe, inda Shugaba Bola Tinubu ya gaje shi.
Har wa'adin mulkin Buhari ya kare, akwai wasu mutane da suke da karfin fada-aji, kuma na kusa da shi da ake zargin su ke juya akalar mulkin kasar.
Yanzu kuwa da tenuwar Buhari ta zama abin tarihi, mun yi nazarin yadda wasu mutum 5 da ake ganin su ne masu ƙarfin fada-aji a gwamnatinsa, kamar yadda The Punch ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Aisha Buhari
Tsohuwar uwargidan shugaban Najeriya ta jajirce wajen fafutukar kare hakkin mata da kananan yara tare da sukar wasu manufofin gwamnatin mijinta.
Bayan barin adar shugaban kasa, Aisha Buhari ta koma birnin Landan domin samun digiri na uku a fannin hulda da kasashen duniya a jami’ar Westminster.
Banda neman ilimi, tana kula da wata kungiyar agaji mai suna Future Assured, wacce ke inganta jin dadi, ilimi, da bunkasa rayuwar mata da matasa.
2. Rotimi Amaechi
Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri ya kasance mai fada a ji a cikin majalisar Shugaba Buhari.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tsarin layin dogo na Najeriya da fadada hanyoyin ruwa da na jiragen sama a lokacin da yake mulki.
A shekarar 2022 ya sauka daga mukaminsa na minista domin neman takarar shugaban kasa a cikin jam’iyyar APC. Duk da kokarin da ya yi, ya samu matsayi na biyu a zaben fidda gwani na jam’iyyar, zaben da ya ba Tinubu nasara.
Yanzu haka dai yana karatun digiri a fannin shari'a a Jami'ar Fatakwal.
3. Abubakar Malami
Abubakar Malami yana da alaka da jam’iyyar APC, kuma ya taka rawar gani wajen nasarar da jam’iyyar ta samu a zabukan 2015 da 2019.
Shugaba Buhari ya nada shi a matsayin antoni janar na gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a a watan Nuwamba 2015 kuma an sake nada shi mukamin a shekarar 2019.
A lokacin da yake rike da mukamin AG na gwamanti, Malami ya tsunduma cikin harkokin shari’a da siyasa daban-daban da suka hada da cin hanci da rashawa da kare hakkin dan Adam da kuma batun tsarin mulki.
Ya kasance wani bangare na kokarin sake fasalin tsarin shari'ar Najeriya don samar da ingantaccen tsarin shari'a.
4. Ibikunle Amosun
Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma sanata sau biyu, wanda ya kasance babban abokin gwagwarmayar Buhari, ya taka rawar gani wajen tabbatar da kawo wa jam’iyyar APC yankin kudu maso yammacin a zaben 2015 da 2019.
Bayan gudummawar da ya bayar a siyasance, ya jagoranci ayyukan samar da ababen more rayuwa daban-daban a jihar Ogun, da suka hada da gina tituna, gadoji, makarantu, da asibitoci.
Bayan kammala wa’adinsa na gwamna karo na biyu a 2019, ya ci gaba da aikinsa a majalisar dattawa, mai wakiltar yankin Ogun ta tsakiya.
5. Tunde Sabiu
Dan uwan shugaba Buhari kuma mai taimaka masa, wanda ya yi fice a harkokin fadar shugaban kasa, ya fuskanci zarge-zargen yin hada-hadar kasuwanci da kwangiloli ba bisa ka'ida ba bisa sahalewar Buhari.
Nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin darakta na hukumar leken asiri ta kasa ya kuma tada hankulan jama'a da kuma saka shakku kan gwamnatin Buhari.
Bayan tafiyar shugaba Buhari daga ofis, an kama Sabiu tare da tuhumarsa da mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba da kuma daruruwan harsashi.
Duk da cewa an bayar da belinsa, daga baya ‘yan sandan sirri sun sake kama shi a harabar kotun, ana ci gaba da shari’a kan tuhumar da ake yi masa.
Gwamnan Najeriya ya dakatar da basarake saboda ya nada sanata sarauta
A wani labarin, gwamnan jihar Gwamnan jihar Anambra ya sauke rawanin sarkin Neni, H.R.H Damian Ezeani saboda ya nada Sanata Ifeanyi Ubah, mai wakiltar Anambra ta Kudu sarautar 'Odejinji Neni'.
Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautun jihar, Tony-Collins Nwabunwanne, ya sanar da dakatarwar a wata wasika da ya aika wa basaraken.
Asali: Legit.ng