Aisha Buhari ta sake sukar salon mulkin mijin ta Muhammadu Buhari

Aisha Buhari ta sake sukar salon mulkin mijin ta Muhammadu Buhari

Uwar gidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a wani salo na dubara ta sake caccakar salon mulkin mai gidan ta, shugaba Muhammadu Buhari a jiya bayan da ta sake yada kalaman adawa da suka na wasu Sanatoci da sukayi ga mijin nata a kafar sadarwar zamanin ta na Tuwita.

Mun samu dai cewa uwargidan ta shugaba Buhari ta yada maganganun Sanata Isah Misau tare da Sanata Ben Bruce ne inda a ciki suke sukar shugaba Buhari game da kashe kashen da ke aukuwa a cikin kasar da ma sauran wasu batutuwan.

Aisha Buhari ta sake sukar salon mulkin mijin ta Muhammadu Buhari
Aisha Buhari ta sake sukar salon mulkin mijin ta Muhammadu Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa kawo yanzu dubban mutane ne suka kalli faya-fayan bidiyoyin da a kafar sadarwar yayin da kuma hakan ke cigaba da haddasa cece-kuce a tsakanin ma'abota anfani da kafar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai uwargidan shugaban kasar ta shiga kafafen yada labarai inda ta soki salon mulkin mijin na ta.

A wani labarin kuma, mun samu cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin ciwo wani sabon bashin da zai kai akalla Naira 315 biliyan zuwa Naira 385 biliyan daga cikin gida a cikin kason farko na wannan shekarar ta 2018.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng