Jigon APC ya Ankarar da Shugaba Tinubu Sirrin Barayi Wajen Satar Dukiyar Gwamnati
- Olatunbosun Oyintiloye ya ba Shugaban kasa shawarar ya kula da kudin tsare-tsaren tallafawa masu karamin karfi
- ‘Dan siyasar ya fadakar da Bola Ahmed Tinubu cewa akwai masu harin wawurar dukiyar da aka ware domin talakawa
- Idan aka yi awon gaba da kudin, Oyintiloye ya ce Bola Tinubu ba zai cin ma nasarar inganta rayuwar al’umma ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Osun - Olatunbosun Oyintiloye wanda yana cikin jagororin APC a jihar Osun, ya yi kira na musamman ga Mai girma Bola Ahmed Tinubu.
The Cable ta rahoto Olatunbosun Oyintiloye yana cewa sai Bola Ahmed Tinubu ya lura da tsare-tsaren da aka kawo domin yaki da talauci.
Dole sai Bola Tinubu ya zura ido
A lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a ranar Lahadi, ‘dan siyasar ya zargi wasu masu son kai da wawurar dukiyar da aka warewa talakawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyintiloye ya ce bai kamata burin shugaban kasa na taimakawa marasa galihu ya gamu da cikas daga wasu masu dogon hannun sata ba.
Jagoran na APC yana ganin zai yi kyau a fito da matakai da za su tabbata cewa tsare-tsaren yaki da talaucin da aka kawo sun amfanar.
Idan ba ayi haka, Punch ta rahoto Oyintiloye yana cewa talaka ba zai ji tasirin gwamnatin da aka rantsar a karshen Mayun 2023 ba.
Kiran Olatunbosun Oyintiloye ga Tinubu
"Mu na da shugaban kasa da yake sa ido a kan duk abubuwan da ake yi a gwamnati, shiyasa mu ka yarda da shi da kyau.
Dole mu mara masa baya kuma mu karfafe shi wajen ganin ya zura ido a kan kudin tallafi domin ayi maganin karkatar da su."
- Olatunbosun Oyintiloye
Yunkurin gwamnatin Bola Tinubu
Vanguard ta rahoto Oyintiloye ya na yabi shugaban kasa ganin yadda aka warewa ma’aikatar jin kai N10bn domin marasa galihu.
Jigon na APC ya ce ana cikin matsi, don haka matakin da Bola Tinubu ya dauka ta karkashin NPRGS zai inganta rayuwar maras hali.
Ina shinkafar da Tinubu ya bada?
Ana da labari Gwamnatin tarayya ta bada umarni a rabawa Sanatoci da ‘Yan majalisa buhunan shinkafa amma ana zargin an boye su.
Bola Ahmed Tinubu ya ce a raba kayan abincin ne domin ragewa talaka radadin cire tallafin fetur wanda ya jawo karin tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng