Assha! Yan Bindiga Sun Kutsa Rukunin Gidaje a Abuja, Sun Sace Mutane 10

Assha! Yan Bindiga Sun Kutsa Rukunin Gidaje a Abuja, Sun Sace Mutane 10

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sanye da kayan Fulani sun dira rukunin gidajen Sagwari da ke Abuja, sun sace mutum 10
  • Yan bindigar sun kai farmakin ne misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi, inda suka yi wa masu gadin wajen dukan tsiya tare da daure su
  • Wani daga cikin wadanda aka sace, ya aika da sakon gaggawa ga mazauna rukunin gidajen kan halin da suke ciki, kafin aka daina jin sa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidaje na 'Sagwari Layout' da ke yankin Dutse, babban birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi, kuma sun sace akalla mutum 10.

A cewar wani da lamarin ya faru kan idonsa, 'yan bindigar sun yi shigar kayan Fulani makiyaya, suka farmaki rukunin gidajen da misalin karfe 7:30 na yamma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake da wani manomi, sun tafka mummunar ɓarna a jihohin arewa 2

Yan bindiga sun sace mutum 10 a Abuja
Yan bindiga sun kutsa rukunin gidaje a Abuja, sun sace mutane 10. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Daga bayanan da The Nation ta tattara, mutum 8 aka sace a rukunin gidajen, sai wasu ma'aikata biyu na wani otel da ke kusa da rukunin gidajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun bi bayan 'yan bindigar don kubutar da mutanen

Wani da aka sace, ya fara aika sakon gaggawa a dandalin mazauna rukunin na WhatsApp, inda ya sanar da su cewa shi da iyalinsa suna cikin hatsari, daga bisani aka ji sa shiru.

Tuni jami'an tsaro tare da hadin guiwar masu gadin rukunin gidajen suka bazama neman mutane a tsaunikan da ke bayan yankin, Leadership ta ruwaito.

An kubutar da wasu masu gadi da 'yan bindigar suka yi wa dukan tsiya tare da daure su a wajen aikinsu.

An kama magidancin da ake zargin ya kashe matarsa a jihar Yobe

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bukaci naira miliyan 60 fansar yara 6 da suka sace a Abuja

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wani magidanci bisa zargin kashe matarsa ta hanyar daba mata wuka a wuya a Damaturu, jihar Yobe.

Wanda ake zargin mai suna Abubakar Musa, ana zargin ya kashe matar ta sa mai suna Ammi Mamman a yammacin ranar Alhamis a lokacin da suke kwance a kan gado.

Kakin rundunar 'yan sanda na jihar Yobe, Dungus Abdulkarim ya ce rundunar za ta gudanar da tsattsauran bincike don gano bakin zaren lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.