Asiri ya tonu: An kama VC na jami'a da ya yiwa daliba cikin shege ya kuma yi mata tsallaken aji

Asiri ya tonu: An kama VC na jami'a da ya yiwa daliba cikin shege ya kuma yi mata tsallaken aji

- Hukumar jami'ar aikin gona ta Michael Okpara ta musanta zargin da ake wa shugaban makarantar na yunkurin cin zarafin wata malama

- Hukumar ta bayyana cewa an ladabtar da malamar ne bayan da tayi tafiya ta bar aiki ba tare da daukar hutu ba

- Shugaban makarantar ya ce a shirye yake don kare kanshi a gaban shari'a ko kuma wata kwamitin bincike da za a iya kafawa

Hukumar jami'ar aikin gona ta Michael Okpara da ke Umudike a jihar Abia ta mayar da martanin zargin shugaban makarantar da ake da lalata da malamar makarantar.

Hukumar makarantar ta musanta aukuwar lamarin kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Asiri ya tonu: An kama VC na jami'a da ya yiwa daliba cikin shege ya kuma yi mata tsallaken aji
Asiri ya tonu: An kama VC na jami'a da ya yiwa daliba cikin shege ya kuma yi mata tsallaken aji
Asali: Facebook

Wata ma'aikaciya mace mai suna Doctor Patricia Mbah ta zargi shugaban makarantar da cin zarafinta, kamar yadda jaridar Drums beat ta ruwaito.

Amma kuma hukumar makarantar ta ce ladabtar da ita kawai aka yi saboda ta yi tafiya zuwa kasar waje ba tare da sanar da hukumar ba kuma ta bar aikinta.

KU KARANTA: Tirkashi: Wani ya mutu a cikin akwatin gawa da fasto ya biyashi ya shiga domin su damfari mutane da mu'ujizar karya

A wata takardar da rijistara da sakataren hukumar suka sa hannu, hukumar makarantar ta kwatanta wannan zargin da aikin fushi da neman fansa.

Ogwu-Agu ya ce bincike ya nuna cewa Farfesa Otunta "a ko ina kuma a kowanne lokaci bai taba cin zarafin Doctor Patricia Mbah ba saboda babu amfanin hakan."

Jami'ar ta jaddada cewa shugaban makarantar a shirye yake da ya kare gaskiyar shi a gaban shari'a ko wata hukumar da za a kafa don bincike.

Wannan martanin daga hukumar makarantar ya zo ne bayan watanni uku da Lakcara a jami'ar jihar Legas, Akoka, Dr. Boniface aka kama shi a wani faifan bidiyo yana bayyana bukatar shi ta kwanciya da wata mai neman gurbin karatu a makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng