Shugaban NANS Na Benin Ya Nemi a Kama Dan Jaridan da Ya Saki Rahoton ‘Digiri Dan Kwatano’

Shugaban NANS Na Benin Ya Nemi a Kama Dan Jaridan da Ya Saki Rahoton ‘Digiri Dan Kwatano’

  • An nemi hukumomin da abin ya shafa su cafke dan jaridar da ya fallasa badakalar takardun digiri a jami'o'in Togo da Benin, Umar Audu
  • Shugaban kungiyar NANS reshen jami'o'in Benin, Ugochukwu Favour ya yi wannan kiran, inda ya ce binciken barazana ne ga gwamnati
  • A cewar Favour, ko da ace gaskiya ne abin da dan jaridar ya ce, sai dai hakan zai diga aya akan hukumar NYSC, hukumar shige da fice ta kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Shugaban daliban Najeriya da ke karatu a jamhuriyar Benin, Ugochukwu Favour ya nemi a kama Umar Audu, dan jaridar da ya fallasa rashin ingancin takardar digiri a jami'ar kasar.

Da ya ke zantawa da Channels TV a ranar Alhamis Favour caccaki dan jaridar kan yadda ya bi wata barauniyar hanya ya sami takardar digiri a Benin ba tare da zuwa makarantar ba.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya 15, 000 sun yi carko-carko da aka dakatar da karbar digirin Benin

An nemi a kama dan jarida Umar Audu
'Digiri dan Kwatano': Shugaban NANS na Benin ya nemi a kama dan jarida Umar Audu Hoto: @Theumar_audu
Asali: Twitter

Allura za ta tono garma, Favour ya gargadi gwamnati da Umar

A cewar Favour:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ka je an buga sitamfi a fasfo dinka, amma ka ki zuwa makarantar. Ba ma wannan ba, shi fa ya yi bautar kasa a 2019, kuma ya sake yi a 2023."

Favour ya yi ikirarin cewar dan jaridar na son gogawa gwamnati kashin kaji, sannan ya diga aya kan fikirar hukumar shige da fice, hukumar NYSC, ya nemi a tuhimi dan jaridar.

Ya ce:

"Ya kamata a kama shi ne, kan dan jarida kana kokarin ballo ruwan da zai iya cinye kowa, tun daga kan gwamnati, NYSC da hukumar shige da fice, za ta shafi kowa."

Binciken dan jarida kan takardun digirin Benin, Togo gaskiya ne?

Ko da aka tambaye shi kan abin da ya kamata ayi bayan fallasar da dan jaridar ya yi wa makarantun kasashen, Favour ya ce:

Kara karanta wannan

Kano: Dan majalisar NNPP ya ba dalibai 512 a mazabarsa kyautar miliyoyin naira, ya gigita jama'a

"Ba wai ina kokonto kan binciken dan jaridar ba, tun da har ya fitar da hujjoji to mai afkuwa ce ta afku.
"Ina ba gwamnatin Najeriya shawara ta gaggauta yin bincike kan wannan lamari, kuma ta dauki matakin da ya kamata."

Wani rahoto na baya bayan ya nuna gwamnatin Najeriya za ta kara yawan adadin makarantun da ta dakatar da karbar takardun digiri din su daga makarantun kasashen waje.

Gwamnati ta dakatar da karbar takardun digiri daga Benin, Togo

Tun da fari, Legit Hausa ta fara ruwaito maku yadda gwamnatin Najeriya ta dakatar da karbar takardar digiri 'yar Togo da jamhuriyar Benin har sai ta gama bincike.

Wannan dakatarwar ta biyo bayan wani rahoto da dan jaridar Daily Nigerian ya fitar, wanda ya nuna ana samun takardar digiri cikin kasa da watanni biyu daga jami'o'in kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel