Najeriya Ta Zama ta 22 da Aka Fitar da Jerin Kasashe Masu Arahar Farashin Fetur a 2024
Nigeria - Rahoton da aka fitar dangane da farashin man fetur a fadin duniya, ya nuna matsayin Najeriya a jeringiyar sauran kasashe.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Bayanan da aka samu a farkon 2024 a wani shafin masu tattara farashin litar fetur ya tabbatar da har gobe mai yana araha a kasar nan.
A mafi yawan kasashe, ana saida litar fetur ne a kan $1.29, ma’ana a farashin Dala a kasuwa, lita ta kai N1, 500 a kasashe da-dama.
Tribune ta ce akwai kasashe da ake sayen fetur a kasa da wannan kudi a gidajen mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bambancin farashin man fetur a duniya
Yawanci kasashe masu arziki sun fi tsadar fetur sai kasashe marasa arziki sosai ko masu danyen mai su ke da rangwamen farashi a duniya.
Kasar da ta fi kowace saukin kudin PMS watau fetur ita ce Iran inda mutane su ke sayen lita a kan %0.029, kusan N26.52 ne a lissafin yau.
A Hong Kong, mutane su ka san saye kowace lita a $3.101 (N2835), a nan ya fi tsada. Birnin na cikin inda ya fi ko ina tsadar rayuwa a duniya.
Fetur: Halin Najeriya da kasashe masu mai
Rahoton ya ce kasashe masu danyen mai kamar Libya, Venezuela, Kuwait da Saudi Arabia akwai araha idan aka kamanta da sauran kasashe.
Duk da kukan da ake yi a Najeriya, lita ta na kimanin $0.722 ne (N660.25) a kudin kasar. NNPC ta musanya zancen yin karin kudi a yanzu.
A Amurka, lita tana kan $0.911 ne a ranar farko a 2024, farashin man fetur a Brazil da Indiya shi ne $1.150 da $1.252 kusan N1, 050 da N1, 144.
Tsadar man fetur a kasashen duniya
1. Iran
2. Libya
3. Venezuela
4. Algeria
5. Kuwait
6. Angola
7. Egypt
8. Turkmenistan
9. Malaysia
10. Bahrain
11. Kazakhstan
12. Bolivia
13. Iraq
14. Qatar
15. Azerbaijan
16. Russia
17. Oman
18. Saudi Arabia
19. Ecuador
20. Sudan
21. Belarus
22. Nigeria
23. UAE
24. Lebanon
25. Kyrgyzstan
26. Argentina
27. Tunisia
28. Paraguay
29. Indonesia
30. Syria
31. Bhutan
32. Panama
33. USA
34. Vietnam
35. Maldives
36. Pakistan
37. Puerto Rico
38. El Salvador
39. Gabon
40. Taiwan
41. Liberia
42. Guyana
43. Colombia
44. Ghana
45. Lesotho
46. Honduras
47. Suriname
48. Afghanistan
49. Guatemala
50. Curacao
51. Uzbekistan
52. Haiti
53. Namibia
54. Swaziland
55. Botswana
56. Dominica
57. Bangladesh
58. Trinidad & Tobago
59. Benin
60. China
61. Brazil
62. Cambodia
63. Zambia
64. Turkey
65. Philippines
66. Australia
67. DR Congo
68. Togo
69. South Korea
70. South Africa
71. Cameroon
72. Canada
73. Japan
74. Georgia
75. Poland
76. Thailand
77. Nepal
78. Tanzania
79. India
80. Cuba
81. Grenada
82. Madagascar
83. Burma
84. Rwanda
85. Dom. Republic
86. Aruba
87. Cape Verde
88. Moldova
89. Fiji
90. Nicaragua
91. Jamaica
92. Saint Lucia
93. Mozambique
94. Laos
95. Kenya
96. Peru
97. Ethiopia
98. N. Macedonia
99. Guinea
100. Bahamas
101. Ukraine
102. Mongolia
103. Bosnia & Herz.
104. Mexico
105. Costa Rica
106. Sri Lanka
107. Burkina Faso
108. Uganda
109. Chile
110. Mali
111. Bulgaria
112. Ivory Coast
113. Malta
114. Cyprus
115. Romania
116. Malawi
117. Andorra
118. Burundi
119. Sierra Leone
120. Slovenia
121. Lithuania
122. Zimbabwe
123. Mauritius
124. Morocco
125. Jordan
126. Seychelles
127. Czech Republic
128. Montenegro
129. Hungary
130. Cayman Islands
131. Austria
132. Luxembourg
133. Croatia
134. Serbia
135. Senegal
136. Spain
137. Latvia
138. Slovakia
139. Sweden
140. Belgium
141. New Zealand
142. UK
143. Estonia
144. Portugal
145. San Marino
146. C. Afr. Rep.
147. Ireland
148. Belize
149. Germany
150. Mayotte
151. Uruguay
152. Wallis and Futuna
153. Italy
154. France
155. Finland
156. Liechtenstein
157. Albania
158. Greece
159. Barbados
160. Switzerland
161. Singapore
162. Israel
163. Netherlands
164. Norway
165. Denmark
166. Iceland
167. Monaco
168. Hong Kong
Matakai bayan cire tallafin fetur
Da aka cire tallafin man fetur, an samu rahoto Gwamnatin tarayya ta dauki matakai domin ragewa talaka radadin tashin farashi.
Bola Tinubu ya yi umarni a ba Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai tirelolin shinkafa da za a raba, amma wasu 'yan siyasar sun boye.
Asali: Legit.ng