Jerin birane guda 11 da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya

Jerin birane guda 11 da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya

An bayyana biranen da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya a wannan shekarar ta 2019. Birnin Paris, Singapore da birnin Hong Kong sunyi kunnen doki ne a matsayin biranen da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya

Babban birnin kasar Faransa, wanda shine yake zuwa na daya a cikin jerin biranen tun daga shekarar 2003 zuwa wannan shekarar da muke ciki, inda a shekarar da ta gabata birnin Hong Kong da yake zuwa na hudu a cikin jerin biranen ya tsallako zuwa na uku.

Binciken da aka yi akan tsadar abubuwa sama da 150 a cikin birane 133 na duniya ya nuna cewa birane uku da suka fi ko ina tsadar rayuwa suna yankin Asia ne da kuma yankin Turai.

1. Paris: Birnin Paris yayi kunnen doki da birane guda biyu, babban birnin kasar Faransan yana zuwa a cikin jerin birane goma mafi tsada a duniya tun daga shekarar 2003 zuwa yanzu.

2. Singapore: Shine birnin da har yanzu bai sakko daga matsayin da yake ba tun a shekarar 2018, birnin Singapore yayi kunnen doki da birnin Paris da Hong Kong.

3. Hong Kong: Ya tsallake birane uku a cikin watanni 12 inda ya shigo cikin jerin birnin Paris da Singapore da suka yi kunnen doki.

4. Zurich, Switzerland: Babban birnin Switzerland shine ya zo a mataki na hudu a cikin jerin birane 133 da aka gabatar da bincike a kansu.

5. Geneva, Switzerland: Banda birnin Zurich, birnin Geneva yana daya daga cikin biranen da suke da tsakar kayan cikin gida, kayan kula da kai da kuma na shakatawa.

KU KARANTA: To fah: Sai nafi kowacce jarumar Kannywood shahara a duniya - Jaruma Maryam MJ

6. Osaka, Japan: Birnin Osaka ya zo mataki na shida a shekarar da ta gabata, kuma yanzu yayi kunnen doki da birnin Geneva na kasar Switzerland.

7. Seoul: Babban birnin Koriya ta Kudu yana daya daga cikin birane hudu a yankin Asiya da suke cikin jerin birane 10 masu tsadar rayuwa.

8. Copenhagen, Denmark: Wannan birnin na yankin Turai an yi binciken yana daya daga cikin biranen da suke da tsadar sufuri.

9. New York: Birnin New York yana daya daga cikin birane biyu na arewacin Amurka da suka shiga cikin jerin birane goman.

10. Tel Aviv: Birni na biyu da yafi kowanne mutane a kasar Isra'ila, wanda yake a mataki na 28 a shekaru biyar da suka gabata, yanzu shine ya dawo na goma a cikin jerin biranen, inda suka yi kunnen doki da birnin Los Angeles.

11. Los Angeles: Birnin Los Angeles da ake kira LA yanzu shine birni na goma da suka yi kunnen doki da birnin Tel Aviv a cikin birane mafi tsada a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng