Tinubu Ya Umarci a Yi Bincike Kan Kudin Tallafin Talakawa N37bn Da Aka Sace a Ofishin Betta Edu

Tinubu Ya Umarci a Yi Bincike Kan Kudin Tallafin Talakawa N37bn Da Aka Sace a Ofishin Betta Edu

  • Gwamnatin Tinubu ta ba da umarnin fara bincike kan zargin karkatar da kudade daga ofishin minsitar jin kai Betta Edu
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka dakatar daya daga cikin manyan jami’an da shugaban ya nada a hukumar hannun jari ta NSIPA
  • Ba sabon abu bane cin amanar gwamnati da yin ganganci da dukiyar al’umma a tsakanin manyan jami’an gwamnatin Najeriya

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarnci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudaden tallafawa talakawa da suka kai N37.1bn daga ofishin ma’aikatar jin mai.

Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu a wata sanarwar da ya fitar, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

A kwanakin baya ne dai shugaba Tinubu ya amince da dakatarwa tare da fara binciken Halima Shehu, Ko’odinetar NSIPA bisa zargin almundahanar kudi kusan Naira biliyan 30.

Tinubu ya umarci a binciken rashawa a ofishin minista Edu
Tinubu ya umarci a bincike kudaden talakawa da aka cinye a ofishin Edu | Hoto: @officialABAT, @edu_betta
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce gwamnati ta kuduri aniyar tono gaskiya dangane da lamarin, kuma ta bada tabbacin daukar matakin da ya dace da zarar an kamala binciken.

Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da gwamnati take binciken wannan zargi tare da tabbatar da gaskiyar da ke ciki.

Gwamnatin Tinubu ta himmatu ga aikata gaskiya

Da yake bayyana matsayar gwamnatin Tinubu game da yiwa 'yan kasa bayani kan duk wani lamari da ake ciki, ministan ya ce:

"Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, tana da nufin nuna gaskiya da rikon amana ga al’umma, kuma ta himmatu wajen ganin an isar da kudaden jama'a garesu kuma an yi amfani da su yadda ya kamata domin magance bukatun ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi dabara 1 da ta dauko domin karya farashin abinci a 2024

"Dangane da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, Shugaban ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike don tabbatar da daidaito da gano gaskiyar abin da aka ruwaito."

Za a binciki ministar Tinubu

A bangare guda, fadar shugaban kasa ta ce tana binciken fitar da kudin tallafin Naira miliyan 585.189 da aka ware wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da Legas zuwa wani asusu.

Wannan dai na zuwa ne zo ne yayin da wasu kungiyoyin fararen hula suka yi kira da a kori ministar harkokin jin kai da kawar da talauci, Dr Betta Edu, saboda ba da umarnin biyan kudin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.