Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Tisa Keyar Babban Basarake
- An samu tashin hankali a yankin Orodo da ke karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, yayin da yan bindiga suka yi awon gaba da mai martaba Eze Samuel Agunwa Ohiri
- Yan bindigar sun sace basaraken ne a gaban gidansa a safiyar Asabar, 6 ga watan Janairu
- An tattaro cewa basaraken, tsohon shugaban sarakunan gargajiya na jihar, na tattaunawa da dan uwansa ne lokacin da yan bindigar suka kawo farmaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Imo - Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Imo, Mai martaba Eze Samuel Agunwa Ohiri.
An rahoto cewa an yi garkuwa da basaraken ne a gaban gidansa da ke Orodo, karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, da misalin karfe 8:30 na safiyar Asabar, 6 ga watan Janairu, rahoton Vanguard.
A cewar wani ganau, yan bindigar sun kuma yi awon gaba da dan uwan Ohiri, wani dan kasuwa da ke zaune a Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A safiyar Asabar, Ohiri da dan uwansa daga Amurka, sun yanke shawarar fita a cikin motarsu yayin bikin Kirsimeti domin ziyartan wasu abokansu. Bayan ziyarar tasu, sun dawo.
"Da isarsu gidan Ohiri, sai suka faka motarsu, a wani gefe na harabar gidan, yayin da su biyun suke tattauna batutuwa na karshe kafin su yi bankwana da juna. Wata motar highlander cike da yan bindiga sun sha gabansu sannan suka yi harbi kan mai uwa da wahabi. Sun dura su duka biyun cikin motar sannan suka yi gaba. Sun yi ta hanyar Njaba zuwa Orlu."
Wani ganau ya ce dan uwan Ohiri, Solomon, ya yi nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da mutanen.
Yan bindiga sun hallaka mutane a Sakkwato
A wani labarin, mun ji cewa a kalla rayuka tara ne suka salwanta yayin da wasu tsagerun ƴan bindiga suka kai farmaki ƙauyuka huɗu a jihar Sakkwato tun daga ranar Litinin har zuwa ranar Talata.
Ganau sun shaida wa Premium Times cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mazauna kauyukan a hare-haren cikin kwanaki biyu kaɗai.
Asali: Legit.ng