Kotu a Kano Ta Bada Umurnin Kama Jami’in Kwastam Kan Kin Amsa Sammacin da Aka Tura Masa

Kotu a Kano Ta Bada Umurnin Kama Jami’in Kwastam Kan Kin Amsa Sammacin da Aka Tura Masa

  • Alkalin kotun musulunci a jihar Kano ya yi umurnin kamo masa wani jami'in kwastam, Yusuf Ismail Mai Biscuit
  • Mai shari'a Garba Malafa ya yi umurnin ne bayan Mai Biscuit ya ki amsa sammacin da aka turawa masa
  • Wani mutum ne dai ya yi karar jami'in kwastam din kan yunkurin da yake na kwace masa gidansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta bayar da umarnin kama wani jami'in kwatsam mai suna Yusuf Ismail Mai Biscuit, bisa kin amsa sammacin da aka tura masa.

Alkalin kotun, Garba Malafa ne ya bayar da umurnin bayan rokon da lauyan mai kara, Idris Saleh Bello ya yi, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

"Kada ka jira har sai sun fara jefe ka": Fitaccen malamin addini ya yi gagarumin gargadi ga Tinubu

Kotu ta yi umurnin kama wani kwastam
Kotu a Kano ta bada umurnin kama jami’in kwastam kan kin amsa ‘sammacin da aka tura masa Hoto: Thisdaylive
Asali: Twitter

Dalilin maka jami'in kwastam din a kotu

Abdullahi Aliyu, wanda ya shigar da karar ya yi zargin cewa Mai Biscuit ya yi barazanar fitar da shi daga gidansa da ke lamba 1,136 C, Layout Kawaji a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ci gaba da zargin cewa jami'in kwastam din ya yi makin bangon gidan nasa da jan fenti sannan ya umurce shi da ya bar gidan nasa, rahoton Punch.

Aliyu ya ce ya mallaki gidan ne ta halastacciyar hanya daga wajen ainahin mai gidan na baya.

Lokacin da aka gabatar da karar a ranar Alhamis, lauyan mai kara, Bello, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ba ya cikin kotu kuma babu wanda ya wakilce shi.

Ya kuma roki kotu da ta yi amfani da karfinta, ta hanyar bayar da umurnin kama wanda ake kara kamar yadda sashe na 352 na ACJL 2019 ya tanada.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

Lauyan ya kara da cewa kotun ta mika wa wanda ake kara sammacin zuwa kotu, inda ya sanar da shi cewa ya bayyana a kotu ranar 4 ga watan Janairu.

"Rashin zuwansa kotu a yau ba tare da kowani dalili ba raina kotu ne wanda yake daidai da aikata laifi," inji lauyan.

Mai aika sammaci ya kuma tabbatarwa da kotun cewa ya kai wa wanda ake kara takardar sammacin kai tsaye. Ya fitar da takardar a matsayin shaidar aiki.

Alkalin kotun ya umarci ‘yan sanda da su kamo wanda ake kara kamar yadda aka bukata.

Ya ce:

"Ko da yake wanda ake tuhuma ba ya cikin kotu kuma ba a wakilci shi ba kuma babu wani dalili da aka bayyana, ma'aikacin kotu ya tabbatar wa kotu cewa ya aika sammacin ga wanda ake tuhuma.
“Wannan shari’ar korafi ne kai tsaye daga lauyan mai kara. Don haka yana da matukar muhimmanci ga wanda ake tuhuma ya halarci kotun.”

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya bayyana dalili 1 da yasa ya amince da yin sulhu a rikicinsa da Wike

Kotun ta tsayar da ranar 8 ga watan Janairu domin sake zama.

An kama masu shafin tsegumi

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya mai yaki da laifuka ta Intanet, ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hada kai da kuma barazana ga rayuwar wata, sakamakon korafin da wata mata mai suna Misis Seye Oladejo ta yi.

Wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta tabbatar da cafke Adebukola Kolapo mai shekaru 27, Nnedum Micheal Somtomchukwu mai shekaru 25 da Isaac Akpokighe mai shekaru 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng