Titin Abuja-Kaduna da Buhari Ya Bada a Kan N165bn Ya Koma N1.35tr – Ministan Tinubu
- David Umahi ya yi zama da darektocin ma’aikatar ayyuka na tarayya, an tattauna game da titin Abuja- Kano
- Ministan ayyukan kasar ya ce akwai sashen da ba a karasa a kan hanyar ba daga birnin Abuja zuwa jihar Kaduna
- Sanata Umahi ya ce kamfanin Julius Berger da aka ba aikin sun dawo suna neman N1.35tr domin su karasa titin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce kamfanin Julius Berger suna bukatar karin kudi domin kammala aikin titin Abuja-Kaduna.
Labari ya zo a Daily Trust cewa Sanata David Umahi ya ce Julius Berger na ikirarin sashen aikin na hanyar Abuja-Kano zai ci masu N1.35tr.
Ministan ayyuka na tarayyan ya yi bayani da ya zauna da darektocinsa a Abuja a ranar Alhamis, ya ce kwangilar ta tashi daga N165bn.
Tarihin kwangilar titin Abuja-Kano
Da farko a kan N165bn Babatunde Fashola ya fara bada aikin, daga baya aka mai da shi N645bn a mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu da aikin ya tashi, David Umahi ya ce gwamnati ba ta da kudin biyan kwangilar.
Shekara 7 ba a gama hanyar Abuja-Kaduna ba
A 2017 aka bada kwangilar sake gina hanyar Abuja zuwa Kano, amma ba a iya fara aikin ba sai cikin shekarar 2018 idan ba a manta ba.
An yi niyyar kammala kwangilar a 2021, amma har Muhammadu Buhari ba a gama ba.
Sai dai an yi nasarar karasa bangaren Zariya zuwa Kano da nufin cewa sannu a hankali za a karasa ragowar sashen Abuja zuwa Kaduna.
Yaushe za a gama titin Abuja-Kaduna a 2024?
The Cable ta ce duk da haka gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana sa ran za a gama gaba daya aikin titin a sabuwar shekarar nan ta 2024.
Ministan ya ce a karkashin tsarin shugaban kasa aka yi aikin bayan an gano kudin sata, ya kuma nuna muhimmancin titin ga yankin Arewa.
Wannan yana cikin manyan ayyukan da aka yi a Najeriya a mulkin Muhammadu Buhari.
Binciken gwamnatin tarayya
An ji labari kungiyar NANS ta Benin ta ce akwai dalibai da ke karatu tsakaninsu da Allah a jami’o’in da aka tsaida karbar takardar shaidarsu.
Kungiyar daliban ta roki gwamnatin Najeriya ta guji yin kudin goro, ta hukunta marasa gaskiya kurum a binciken masu digirin bogin waje.
Asali: Legit.ng