Sojojin Sama Sun Kashe Shugaban Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa, da Wasu Mayakansa a Borno

Sojojin Sama Sun Kashe Shugaban Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa, da Wasu Mayakansa a Borno

  • Luguden wutan jirgin sojojin Najeriya ya halaka shugaban ISWAP, Ba'a Shuwa da wasu mayaƙansa a jihar Borno
  • Zagazola Makama ya ce sojoji sun sami wannan nasara ne yayin wani samame da suka kai ranar 2 ga watan Janairu, 2024
  • Shuwa ya hau kujerar shugabanci ne bayan Abubakar Sheƙau ya bindige kansa a 2021, kuma yana da manyan kwamandoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe shugaban ƙungiyar ta'addanci ISWAP, Ba'a Shuwa, da gomman mayaƙansa a jihar Borno

Sojojin sun halaka ƙasurgumin ɗan ta'addan ne yayin wani liguden wuta da suka yi a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ranar 2 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

Jirgin soji ya yi ajalin jagoran ISWAP.
Ruwan Bama-Baman Sojoji Ya Sheke Jagoran Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa da Mayakansa Hoto: ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Ba’a Shuwa, shi ne jagoran ISWAP na Wylayat Najeriya, Tafkin Chadi, Kwalfarji da Timbuktu Farouq da kuma Sambisa Mantika mai dangantaka da kungiyar ISIS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi ne ya tabbatar da kisan jagoran ƴan ta'addan a shafinsa na manhajar X.

Ya ce majiyoyi masu tushe sun shaida masa cewa jirgin sojin sama ya yi ruwan wuta a Kwatan Dila, ƙaramar hukumar Abadam, jihar Borno ranar 2 ga watan Janairu.

A cewarsa, "wannan luguden jirgin sojin ne ya yi ajalin jagoran ISWAP, Ba'a Shuwa tare da ɗumbin mayaƙansa."

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa bayan samamen sojojin, wani faifan bidiyo ya nuna yadda luguden ya murƙushe yan ta'addan da dukkan kayan aikinsu.

Yadda Shuwa ya zama shugaban ISWAP

An naɗa Shuwa a matsayin jagoran kungiyar ƴan ta'addan ne a shekarar 2021 bayan Abubakar Sheƙau, shugaban Boko Haram ya kashe kansa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, fitaccen jarumin fim ya mutu a Najeriya

Ya kasance Kwamandan ‘yan ta’adda a Chiralia, Markas Kauwa, Abirma, Buk, Abulam, Dusula, Abbagajiri, Gorgore da sauran sansanoni da dama a yankin Timbuktu da Alagarno a Kudancin Borno.

Ba’a Shuwa da tawagarsa ne suka fi kai hare-hare, kwanton bauna da dasa nakiyoyi a titunan Damboa, Damaturu-Maiduguri, Askira, Buratai, Buni Yadi, Buni Gari, Gaidam da sauran sassan jihohin Borno da Yobe.

Wasu daga cikin manyan kwamandojinsa sun haɗa da; Khaid Hanzala, Ba'a Idirisa, Rawana, Abou Ibrahim, Malam Abubakar, Abou Aisha da Abou Khalid wanda ya dauki alhakin harin kan layukan wutar lantarki.

Yan bindiga sun kai sabon hari a Zamfara

A wani rahoton kuma 'Yan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Kwanar Dutse a jihar Zamfara saboda sun gaza biyan harajin N20m.

Wani mazaunin garin ya ce 'yan ta'addan sun kashe mutum 10 jim kaɗan bayan kammala sallar la'asar ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262