An Kama Wata ‘Kwararriyar’ Barauniyar Waya da Wasu Mutum 84 a Borno, Ta Bayyana Yadda Ta Ke Takunta
- 'Yan sanda sun cafke wata wata wacce ta kware wurin sata da kwacen waya a birnin Maiduguri
- Wacce ake zargin mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' an cafke ta ne tare da wasu mutane 84 kan zargin wasu laifuka
- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Daso Nahum ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 4 ga watan Janairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - Rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta cafke wata mata kwararriyar mai kwacen waya a Maiduguri.
Wacce ake zargin mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' ta shiga hannu da wasu mutane 84, cewar Daily Trust.
Mene ake zargin matar da aikatawa a Borno?
Sauran mutanen da aka kaman ana zarginsu da aikata laifuka da dama da suka hada da mallakar makamai da fashi da kisan kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin gabatar da masu laifin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Daso Nahum ya ce sun aikata da laifukan ne daga 1 ga watan Oktoba zuwa 31 ga watan Disamba.
Nahum ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 4 ga watan Janairu a Maiduguri babban birnin jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Mene rundunar ta ce kan wacce ake zargin?
Kakakin ya ce Bintu wacce ke zaune a unguwar Shehuri a cikin Maiduguri ta shiga hannu a ranar 28 ga watan Disamba.
Ya ce:
"Yayin binciken Bintu ta bayyana sunan wani Mohammed Isa da ke Babban Layi da suke harkar tare.
"Yadda su ke aikata satar shi ne zuwa gidajen mutane a matsayin masu aiki inda suke sace wayoyinsu."
Tirela ta murkushe sabon dan sanda a Jigawa
A wani labarin, wani matashin dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan tirela ta murkushe shi a jihar Jigawa.
Marigayin mai suna Abba Safiyanu an tabbatar da cewa sabon shiga aikin dan sanda ne wanda aka tura jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ringim da ke jihar a ranar Talata 2 ga watan Janairu da yammacin ranar ta wannan mako da muke ciki.
Asali: Legit.ng