An Kama Yan Arewa Da Ke Kokarin Shiga Aikin Soja Karkashin Jihar Legas

An Kama Yan Arewa Da Ke Kokarin Shiga Aikin Soja Karkashin Jihar Legas

  • Wasu matasa shida daga jihar Kaduna za su fuskanci fushin gwamnatin jihar Legas kan takardun bogi
  • Matasan kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun yi amfani da takardun zama 'yan Legas don samun aikin sojin Najeriya
  • Sai dai, bayan wani bidiyo da ya yadu na yadda aka gano ba 'yan asalin jihar Legas ba ne, gwamnatin jihar ta dauki mataki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Gwamnatin jihar Legas ta ba da umunin gurfanar da wasu 'yan Arewa 6 da suka yi karyar su 'yan asalin jihar ne a wajen neman aikin soja.

Wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba ya nuna matasan 'yan asalin jihar Kaduna, suna ikirarin sun fito daga kananan hukumomin Kosofe, Lagos Island da Oshodi na jihar Legas ne.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta 2 daga aiki, za ta gurfanar da su gaban kotu, ta fadi dalili

Daukar aikin soja
An kama 'yan Arewa da ke kokarin higa aikin soja karkashin jihar Legas
Asali: Twitter

Da ya ke zantawa da jaridar The Punch a ranar Laraba, kwamishinan watsa labarai na jihar Legas, Mr Gbenga Omotoso ya ce tuni aka kai karar matasan ga gwamnatin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika ya ce an ba 'yan sanda damar cafke duk wanda aka kama yana amfani da takardun bogi na zama ɗan asalin jihar Legas alhalin ba dan jihar ba ne.

Laifi ne amfani da takardar bogi ta shaidar zama dan jihar Legas

Mr Omotoso ya ce:

"Ba mu samu wannan rahoton ba tukunna. Amma laifi ne ikirarin kai dan jihar Legas ne alhalin ba haka ba ne, 'yan sanda za su kama irin mutanen nan.
"Kuma wannan sojan gonar, laifi ne da za a iya hukunta mutum karkashin dokar kasa ta jihar Legas."

Matasan shida sun yi nufin amfani da shaidar zama 'yan jihar Legas don samun damar shiga aikin soja a guraben da aka ware wa jihar, kuma rundunar soji ta kama su, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Na kusa da gwamnan PDP ya ɗauki matakin karshe kan ƴan majalisa 25 da suka koma APC

Bidiyon ya jawo cece kuce musamman a tsakanin 'yan asalin jihar Legas, inda wasu ke ikirarin ana kwace guraben da ake ba Legas ta wannan hanyar.

Rahon jaridar The Cable ya nuna cewa rundunar soji ta ce bidiyon ya nuna yadda rundunar ke kokarin yin adalci da bin matakai wajen daukar aikin soji a kasar.

Me ya sa ake son bata sunan 'yan Arewa?

Wani Shamsudden Lawal mazaunin Abuja, da ya ke martani kan wannan batu, ya koka kan yadda duk wani laifi ake dora shi a kan 'yan arewa kawai.

Malam Lawal ya ce:

"Ko a Arewa akwai 'yan Kudu da ake aiki da takardun shaidar su 'yan Arewa ne, hatta a siyasa akwai dan Kudu da ya nemi takara a nan Arewa, amma mu ba mu yi korafi ba?
"Ko a ma'aikatu, ko aikin tsaro, za ka ga 'yan Kudu sun nemi aiki kuma sun samu da takardun Arewa, amma yau saboda an kama 'yan Kaduna shida, ake yamididi da 'yan Arewa."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Shi kuwa Umar Ali Dangata mazaunin garin Jos, jihar Filato, cewa ya yi:

"Wannan sai ya zama izina ga 'yan Arewa, mu dawo mu gya shiyyarmu tunda duk inda muka je ana kyararmu.
"Idan kuwa gaskiya za a fada, ba za mu iya lissafa Yarbawa ko Inyamurai nawa ne suke aiki a Arewa da takardun shaidar su 'yan Arewa ne, amma ba mu dauki mataki akai ba."

An gano sinadarin da ke haifar da sankarar bargo a man fetur

Wani kwararren likitan jini, Dokta Oladapo Aworanti ya gargadi 'yan Najeriya da su rage yawan mu'amala da man fetur da magungunan kashe kwari.

A cewar Dokta Aworanti akwai sinadarin Benzene a cikin man fetur ke haifar da cutar sankarar bargo wacce ke iya kashe mutum idan ba a dauki mataki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.