"Ta Yaya Ta Aikata Hakan?": Matashiyar Budurwa Ta Yi Amfani Da Takardun Bogi Wajen Siyo Dalleliyar Motar N8m

"Ta Yaya Ta Aikata Hakan?": Matashiyar Budurwa Ta Yi Amfani Da Takardun Bogi Wajen Siyo Dalleliyar Motar N8m

  • An yankewa wata budurwa ƴar Limpopo tarar R10 000 (₦242,780.16) ko zaman gidan kaso na shekara biyu, bisa siyan mota ƙirar Hyundai Atos
  • Budurwar mai shekara 22 ta shiga hannun hukuma ne bisa zargin damfara, bayan ta miƙa takardun bogi ga bankin Wesbank domin samo kuɗin siyan mota
  • Mutane da dama sun yi mamakin yadda ta iya kitsa wannan aika-aikar ba a ganota ba, yayin da wasu ke cewa jami'in bankin shi ma ya cancanci hukunci

POLOKWANE - Wata budurwa mai shekara 22 daga Limpopo ta gamu da fushin hukuma, bayan an yanke mata hukuncin tarar R10 000 (₦242,780.16) ko zama gidan gyaran hali na shekara biyu bayan an kama ta da laifin damfara.

Kakakin jami'an Hawks, Laftanar Kanal Matimba Maluleke, ya ce budurwar ta yi amfani da takardun bogi wajen siyan mota ƙirar Hyundai Atos, wacce kuɗinta sun kai sama da R340 000 (₦8,141,425.23).

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Matashiyar budurwa ta siyo motar N8m da takardun bogi
Ta yi amfani da takardun bogi wajen siyan Hyundai Atos Hotos: Thawornnukar, @Auction_finance
Asali: UGC

Budurwar ta yi amfani da takardun bogi wajen samo kuɗin siyan motar

A cewar rahoton IOL, an yankewa budurwar mai suna Miranda Thandaza Lubisi, hukunci ne a ranar Juma'a 12 ga watan Mayu, a kotun laifuffuka na musamman ta Polokwane.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matimba ya yi bayanin cewa Lubisi ta je wajen wani dillalin motoci ne a Tzaneen, domin siyan mota a watan Satumban 2022.

Daga nan sai ta nemi samun kuɗin siyan mota tare da taimakon wani mai siye da siyarwa, amma sai ta bayar da takardun bogi ga bankin Wesbank.

Bankin ya amince da kuɗin siyan motan da ta je nema, inda aka bata motar.

An gano wannan damfarar da ta aikata ne wasu ƴan watanni daga baya, lokacin da bankin ya ke bin diddigin harkokinsa, inda aka gano cewa ba gaskiya a cikin takardun da ta kawo bankin.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

An shigar da ƙorafin aikata zamba a ofishin ƴan sanda na Tzaneen, wanda daga baya aka tura shi zuwa wajen jami'an Hawks.

A cewar shafin yanar gizo na SAPS, bayan tarar da aka ƙaƙaba mata, an kuma yanke mata hukuncin shekara biyar a gidan kaso wanda ba za ta yi ba, idan har ba ta sake aikata irin wannan laifin ba, a tsawon lokacin.

Attajirin Matashi Ya Bayar Cigiyar Tsohon Dutsen Guga, Zai Biya Makuden Kudi

A wani labarin na daban kuma, wani attajirin matashi ya bazama cigiyar wani tsohon dutsen guga da zamaninsa ya wuce.

Matashin ya bayyana cewa a shirye ya ke ya gwangwaje duk wanda ya samo masa wannan dutsen gugan, da maƙudan kuɗade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel