Allahu Akbar: Limamin Masallacin Amurka da Aka Harba da Bindiga Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Allahu Akbar: Limamin Masallacin Amurka da Aka Harba da Bindiga Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Limamin masallaci a New Jersey da aka harba da bindiga ya rigamu gidan gaskiya a ranar Laraba, kamar yadda hukumar jihar ta sanar
  • Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Talatar da ta gabata ne aka harbi Hassan Sharif a wurare daban daban a jikinsa a harabar masallacin
  • Sai dai mahukuntan jihar sun tabbatar da cewa kisan limamin bai yi kama da na bambancin addini ba, amma suna bincike a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Antoni Janar na New Jersey ya sanar da rasuwar limamin masallacin New Jersey da aka harba da bindiga a ranar Laraba, inda ya ce ba kisan bambancin addini ba ne.

An harbi Hassan Sharif a wurare daban-daban a jikinsa a harabar masallacin da ke Newark, yamma da New York, inda ya mutu jim kadan bayan kai shi asibiti.

Kara karanta wannan

Miyagu sun harbe babban limamin Masallacin Jumu'a da ɗan acaɓa a Filato

Limamin masallacin Amurka da aka harba da bindiga ya rasu
Limamin masallacin Amurka, Hassan Sharif da aka harba da bindiga ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Facebook/Hassan Sharif
Asali: UGC

Ba bambancin addini ya sa aka harbe limamin ba - Platkin

Jaridar VOA ta ruwaito Antoni Janar Matt Platkin na bayanin :

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har yanzu ba mu san dalilin kashe limamin ba, amma dai ga dukkan alamu, harin ba na bambancin addini ba ne, muna kan gudanar da bincike."

Ya kara da cewa:

"La'akari da abubuwan da ke faruwa a duniya, ana samun rikicin addini a jihar New Jersey, musamman ya fi shafar Musulmai, wanda ke zaman dar-dar a halin yanzu."

Matt Platkin ya ce akwai akalla Musulmi dubu 300 a jihar, kuma 'yan asalin Amurka.

Abin da hukumomin New Jersey ke cewa game da Hassan Sharif

Tun bayan barkewar fada tsakanin Isra'ila da Hamas, aka samu karuwar yawaitar kai hare-hare kan Musulmi a Amurka, a cewar wani rahoto na jaridar Reuters.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Jami'in shigar da kara na jihar, Ted Stephens ya tabbatar da cewa an har limamin fiye da sau daya, inda ya ce"

"Za mu tabbatar mun hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin, kuma mu sakawa iyalan limamin."

Hukumar kula da harkokin addinin Islama a Amurka reshen jihar New Jersey (CAIR-NJ), sun nuna kaduwarsu kan harbe limamin da mutuwarsa, Foexnews ta ruwaito.

Yan bindiga sun kashe dan sanda, sun sace fasinjoji a jihar Anambra

A nan kasa Najeriya kuwa, wasu 'yan bindiga sun farmaki Uga da ke karamar hukumar Aguata da ke jihar Anambra, inda suka kashe dan bindiga.

A yayin farmakin, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun yi awon gaba da wasu da dama da ke hanyar dawowa daga bukukuwan Kirsimeti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.