Gwamnatin Tinubu Za Ta Kara Dakatar da Karbar Digiri Daga Wasu Kasashe Bayan Benin da Togo

Gwamnatin Tinubu Za Ta Kara Dakatar da Karbar Digiri Daga Wasu Kasashe Bayan Benin da Togo

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na ƙara tsawaita dakatar da tantancewa da karɓr takardun shaidar digiri daga ƙasashen Uganda, Kenya da Jamhuriyar Nijar
  • Hakan dai ya biyo bayan rahoton binciken da wani ɗan jarida ya bayar kan yadda ya samu digiri a wata jami’a a jamhuriyar Benin cikin ƙasa da watanni biyu
  • A ranar Talata 2 ga watan Janairu ne gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da tantancewa da kuma tabbatar da shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A yayin da ake fama ƙaruwar jami'o'i masu bayar da digirin bogi a Afirika, gwamnatin Bola Tinubu ta ce za a ƙara sanya takunkumi ga ƙasashe kamar Kenya, Uganda, da Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara binciken minista kan badakalar N585.2m

FG za ta dakatar da karbar digiri daga wasu kasashen Afirika
Gwamnatin tarayya za ta dakatar da karbar digiri daga kasashen Kenya, Uganda da sauransu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan ya biyo bayan dakatar da tantancewa da amincewa da takardun shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo bayan wata fallasa da ta tona asirin wasu jami'o'i a Cotonou.

Ministan ilmi na Najeriya, Tahir Mamman, ya bayyana matsayar gwamnatin tarayya kan Kenya da Uganda yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a yammacin Laraba, 3 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ba za mu tsaya a Benin da Togo kawai ba. Za mu ƙara tsawaita dakatarwar zuwa ƙasashe kamar Uganda, Kenya, har da Nijar.
"Za mu tsawaita dakatarwar zuwa wasu ƙasashen da irin waɗannan jami'o'in ke aiki."

Ku kalli hirar a nan ƙasa:

Legit Hausa ta samu jin ta bakin Zaharaddeen Hamisu, malami a Ƙwalejin Sardauna College and Islamic Studies, wanda ya yaba da matakin da gwamnatin tarayyar ta ɗauka.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana dalilin da ya sa ba za a kira gwamnatin Buhari matsayin wacce ta gaza ba

Malamin ya yi kiran da gwamnatin ta gudanar da bincike domin tantance sahihan makarantu waɗanda ba su wannan baƙar sana'ar ta bayar da digirin bogi.

A kalamansa:

"Matakin da gwamnati ta dauka na dakatar da digiri ɗan kwatano abu ne mai kyau, sai dai ya kamata gwamnati ta bincika don tantance sahihan makarantu, waɗanda suka cika ƙa'ida a ƙasashen domin ba su damar cigaba da gudanar da harkokinsu."

N600k kacal na kashe na samu digirin bogi, ɗan jarida

Umar Shehu Audu ɗan jaridar da ya fallasa yadda ake samun digiri na bogi daga Jamhuriyar Benin, ya bayyana cewa N600k kawai ya kashe ya samu ƙwalin digirin.

Umar ya bayyana cewa bai taɓa shiga aji ba ko ta ya taka ƙafarsa zuwa harabar jam'iyyar, ballantana har ya kai ga rubuta jarabawa.

Shugaban ICPC Ya Gana da Ɗan Jaridar da Ya Yi Fallasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ya sanya labule da ɗan jaridar da ya fallasa yadda ake samun digirin bogi a Jamhuriyar Benin.

Shugaban na ICPC ya gana da Umar Shehu Audu domin samun ƙarin bayanai kan yadda wannan kasuwar ta digirin bogi take gudana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng