Babban Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Damana Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya karbi rayuwar Sheikh Usman Abubakar Damana a yau Laraba 3 ga watan Janairu a jihar Kebbi
- Damana kafin rasuwarshi, shi ne babban limamin masallacin Juma'an Geese Phase 1 da ke birnin Kebbi
- Za a gabatar da sallar jana'izarshi a masallacin Juma'an Geese Phase 1 da ke birnin Kebbi da misalin karfe biyu na rana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Da safiyar yau Laraba ce aka samu labarin rasuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Kebbi.
Marigayi Sheikh Usman Abubakar Damana ya rasu a yau Laraba 3 ga watan Janairu a birnin Kebbi, cewar Dokin Karfe TV.
Waye ne Sheikh Usman Damana a Kebbi?
Kafin rasuwarshi, shi ne babban limamin masallacin Juma'an Geese Phase 1 da ke birnin Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, shi ne mataimaki na biyu a kungiyar Izala a jihar Kebbi baki daya, cewar JIBWIS Gombe.
Za a gabatar da sallar jana'izarshi a masallacin Juma'an Geese Phase 1 da ke birnin Kebbi da misalin karfe biyu na rana.
Mutuwar malamin ta daga hankulan mutane ganin irin gudunmawar da ya bai wa addinin Musulunci a harkar karatuttukansa
Mutuwar Sheikh Giro ta girgiza al'ummar Musulmai
Wata majiya ta tabbatar da cewa a jiya ma sai da malamin ya gudanar da karatu da ya saba yi tsakanin mangariba da isha.
Har ila yau, Allah ya karbi rayuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Kebbi, Sheikh Abubakar Giro Argungu.
Giro ya rasu ne a watan Satumba bayan fama da jinya na tsawon lokaci a birnin Kebbi da ke jihar.
Mutuwar malamin ta girgiza al'ummar Musulmai a kasar baki daya ganin irin gudunmawar da ya bayar a ci gaban Musulunci.
Babban limami ya rasu a Gombe
A wani labarin, Babban limamin masallacin Juma'a a Unguwar Abuja da ke birnin Gombe ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin Sheikh Imam Sa'idu Abubakar ya rasu a birnin Gombe bayan dama da jinya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi inda ya tura sakon jaje ga iyalan mamacin.
Asali: Legit.ng