NNPC Na Rikici da ‘Yan Kasuwa, Ana Zancen Litar Fetur Ta Haura N1200 a Kasuwa
- ‘Yan kasuwa sun ce a yadda farashin danyen mai yake a duniya, ba za ta yi wu a saida fetur a kan N600 ba
- Har yanzu mutanen Najeriya suna sayen man fetur ne a kan N617-N690, duk da ikirarin cire tallafi tun tuni
- Kamfanin mai na NNPCL ya hakikance cewa an yi waje da tsarin tallafi, ‘yan kasuwa sun karyata wannan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kamfanin mai na kasa wanda aka fi sani da NNPCL ya samu sabani da ‘yan kasuwan da ke karkashin kungiyar IPMAN.
A ranar Laraba, Punch ta kawo labari cewa ana gardama a kan cire tallafin fetur da shugaba Bola Tinubu ya yi daga hawa mulki.
...ana biyan tallafin man fetur?
Muddin farashin fetur bai tashi ba, masana tattalin arziki sun ce an dawo da biyan tallafi, zargin da tuni kamfanin NNPCL ya karyata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan kasuwa sun shaidawa Punch cewa la’akari da karyewar da Naira ta ke cigaba da yi a yanzu, ba za a iya saida fetur a N600 ko N700 ba.
Bayan tashin Dalar Amurka a kan Naira, farashin gangar mai ya karu saboda haka ake hasashen gaskiyar lita ta kai N1, 200 a kasuwa.
Nawa fetur yake a Najeriya?
Ana saida fetur a gidajen mai ne tsakanin N617 zuwa N690 a jihohin Najeriya a yanzu.
Wani matafiyi ya shaida mana ya saye lita kusan 30 ne a kan fiye da N20, 000 a Bauchi. A wasu gidajen mai a Kaduna lita tana N670.
Ba a gama cire tallafin fetur ba
Dr. Muda Yusuf ya ce gwamnati tana biyan wani bangare na tallafin man fetur har yanzu.
Masanin tattalin yana ganin gwamnatin Bola Tinubu ta dauki matsayar ne saboda halin tattalin arziki, zamantakewa da siyasa.
Cif Ukadike Chinedu a lissafinsa ya ce litar fetur ta kai tsakanin $2.99 zuwa $3.15 a kasashen waje, hakan ya nuna tallafi bai tafi ba.
Tsare-tsare za su jawo fetur ya tashi
Baya ga janye tsarin tallafin fetur, sabon shugaban Najeriyan ya jawo bankin CBN ya daidaita farashin kudin kasashen waje a 2023.
A makon nan an saida Dala a bankuna a kan N998 sai kuma N1, 225 a kasuwar canji, hakan zai yi sanadiyyar tashin litar man fetur.
Asali: Legit.ng