Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Kauyen Neja, Sun Sace Mata Da Miji Da Karamin Yaro
- Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Garam da ke jihar Neja inda suka yi garkuwa da mutum uku
- Wannan na zuwa kasa da mako daya da 'yan bindigar suka kai farmaki kauyen wanda ya yi silar mutuwar mutum daya
- A wannan farmakin na ranar Talata, 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wani, inda suka tafi da miji da mata da karamin yaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Neja - Yan bindiga sun sake afkawa kauyen Garam da ke jihar Neja wanda makwaftaka da birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da mata da miji tare da karamin yaro.
Wani mazaunin Garam, Lucky Barnabas, wanda ya tabbatar da faruwar sabon harin, ya ce 'yan bindigar sun kai farmakin misalin karfe 12:13 na safiyar ranar Talata.
Ya ce ‘yan bindigar wadanda suka zo a gommansu dauke da bindigu kirar AK-47, sun yi harbin kan mai uwa da wabi domin saka tsoro a tsakanin mazauna garin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karo na biyu da 'yan bindiga na kai hari garin Garam
Daily Trust ta ruwaito ta ce ‘yan bindigar sun tafi da wani mutum da matarsa da kuma wani karamin yaro da ke zaune tare da su.
Barnabas ya ce:
"Ba mu iya yin barci a daren jiya ba yayin da ‘yan bindigar suka sake dawowa bayan mako guda da zuwansu inda suka kashe mutum daya da yin awon gaba da mutum hudu."
Kawo yanzu dai babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan jihar Neja kan lamarin, sai dai mazauna yankin sun ce wasu jami’an soji sun isa yankin jim kadan da faruwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun bi sahun barayin, amma sun kasa ceto wadanda aka sace.
Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a jihar Nasarawa
A wani labarin makamancin wannan, 'yan bindiga sun sace shugaban karamar hukumar Akwanga, Safiyani Isah da wani Alhaji Adamu a jihar Nasarawa.
Rundunar 'yan sanda tare da jami'an tsaro na iya bakin kokarin su don ganin sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng