Yan Bindiga Sun Harbe Dan Banga, Sun Yi Garkuwa da Mutum 3 a Babban Birnin Tarayya Abuja
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku bayan harbe wani dan banga a Bwari da ke Abuja
- Wani mazaunin garin da abin ya faru a idonsa, ya shaidawa manema labarai cewa 'yan bindigar sun dira garin a safiyar Litinin
- Ya ce akwai alamar sun zo garin ne don farmakar gidan wani Ishaya Markus, inda a nan ne suka yi awon gaba da mutum uku
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bwari, Abuja - ‘Yan bindiga sun harbe wani dan banga mai suna Samson tare da yin garkuwa da mutum uku a Barangoni da ke gundumar Bwari da ke birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin Barangoni mai suna Joshua Madaki ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda ‘yan bindigar suka mamaye yankin.
Abin da ya faru a garin Barangoni na harin 'yan bindigar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan wani Ishaya Markus ne bayan da suka samu shiga ta kofar baya inda suka yi awon gaba da mutanen uku da suka samu a gidan.
Madaki ya ce ’yan banga da ke sintiri sun kai dauki wurin, sai dai daya daga cikin ‘yan fashin ya bude wuta da ganin ‘yan bangan inda ya jikkata daya daga cikinsu, rahoton Daily Trust.
Ya kuma shaida cewa an garzaya da dan bangan da ya samu rauni a cinyarsa zuwa asibiti da ke yankin domin yi masa magani.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine ya ci tura, har zuwa lokacin gabatar da rahoton.
Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukumar jihar Nasarawa
A safiyar yau, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa wasu 'yan bindiga sun sace shugaban karamar hukumar Akonga, Safiyanu Isa Andaha da ke jihar Nasarawa.
An ruwaito cewa an yi garkuwa da Mr Andaha da wani Alhaji Adamu a kan hanyar Akonga zuwa Andaha, amma yan sanda sun bazama neman 'yan bindigar.
Asali: Legit.ng