“Mutane Na Zaman Jira”: Ango Ya Fasa Aurensa Yan Awanni Kafin Biki, Ko’ina Ya Hargitse

“Mutane Na Zaman Jira”: Ango Ya Fasa Aurensa Yan Awanni Kafin Biki, Ko’ina Ya Hargitse

  • An zargi wani ango da fasa aurensa da sahibarsa wacce suka kwashe kimanin shekara guda suna shan soyayya
  • Masoyan biyu sun shirya gudanar da shagalin kafin aurensu a ranar 22 ga watan Disamba, amma sai angon ya fasa auren yan awanni kafin shagalin bikin, cewa bai shirya ba
  • Wata majiya ta kusa da amaryar ta sanar da cewar budurwar angon wacce ta haifa masa da ta dawo, don haka wannan ne dalilinsa na daukar matakin
  • Mahaifiyar amaryar ta sume bayan ta samu labarin mai gigitarwa sannan aka kwasheta zuwa asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wasu iyali a kauyen Sokyot, gudunmar Kipkaren da ke mazanar Mosop, Nandi sun samu karayar zuciya bayan angon diyarsu ya fasa aurensu ana gab da biki.

Kara karanta wannan

Maganar aure na rawa bayan saurayi ya sa budurwa ta girkawa danginsa su 70 abinci, gishiri ya zarce

Ango ya fasa auren amaryarsa ana gaba da biki
“Mutane Na Zaman Jira”: Ango Ya Fasa Aurensa Yan Awanni Kafin Biki, Ko’ina Ya Hargitse Hoto: Prostock-Studio, fstop123.
Asali: UGC

Dalilin da yasa angon ya fasa auren

Da take zantawa da kafar labarai ta kasar Kenya, TUKO.co.ke, wata yar kauyen su amaryar ta bayyana cewa masoyan sun shirya gudanar da shagalin kafin bikinsu a ranar 22 ga watan Disamba, amma hakan bai samu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An shirya komai da kyau, kuma mutane na ta jiran zuwa babban ranar. Amma a ranar 21 ga watan Disamba, sai angon ya aikawa amaryar sako yana fada mata cewar ya fasa auren. Ya ce shi bai shirya ba kuma ya canja shawararsa," inji ta.

Abun da angon ya aikata a baya ne ke bibiyarsa

Majiyar ta yi zargin cewa mahaifiyar angon na kaunar budurwar da suka haihu da shi, kuma ta dawo yan awanni kafin aurensa da daya matar.

"Amaryar ma ta haihu da angon, da samun labarin, mahaifiyar ta kadu, ta yanke jiki ta fadi, inda aka kwashe ta zuwa asibiti."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan gida daya su 8 sun mutu a hatsarin mota yayin zuwa bikin sabuwar shekara

Angon wanda ya fito daga tsaunin Nandi, yana ta sauya hotunan shafinsa na Facebook kuma ga dukkan alamu abun da ya faru bai dame shi ba.

Wani mutum ya fasa auren budurwarsa

A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa ‘yar Najeriya ta shiga kunci yayin da saurayin da za ta aure ya ce sam ya fasa, ya soke aurensu.

A cewar wani bidiyon da ya yadu a kafar Faccebook, mutumin da zai auri budurwar ya gano yadda ta kai ziyarar karshe wurin wani tsohon saurayinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng