‘Yan Bindiga Sun Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 7 Kan ‘Yan matan Jami’ar Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 7 Kan ‘Yan matan Jami’ar Zamfara

  • ‘Yan bindiga sun yi barazanar kashe wasu daga cikin daliban jami’ar FUG da aka dauke watanni da su ka wuce
  • Iyayen daliban jami’ar ta Gusau sun roki gwamnatin Najeriya ta sa baki domin yaransu su dawo gida cikin lafiya
  • Miyagun ‘yan ta’addan sun ce nan da mako guda za a kashe daliban idan ba a fito da mutanensu da ke tsare ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - Iyayen daliban jami’ar Gusau watau FUG da ke jihar Zamfara, sun kai kukansu zuwa gaban gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Wadannan Bayin Allah sun roki gwamnatin tarayya ta ceto ‘ya ‘yansu kafin su zama tarihi, Daily Trust ta fitar da rahoton a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, sun sace fasinjojin da suka tafi hutun Kirsimeti

'Yan bindiga
'Yan bindiga sun addabi Gusau Hoto: www.fugusau.edu.ng
Asali: UGC

Iyayen yaran Gusau sun roki gwamnati

Iyayen sun nemi gwamnati ta tattauna da ‘yan bindigan da suka dauke ‘ya ‘yansu kamar yadda aka yi da irinsu Boko Haram a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis dinnan iyayen suka yi wannan roko bayan bidiyoo ya bayyana, inda aka ji ‘yan ta’addan suna barazanar kashe yaransu.

Idan har ba a iya biya masu bukatunsu ba, miyagun ‘yan bindigan sun yi alkawarin hallaka wasu daga cikin ‘yan matan da su ka dauke.

Jaridar ta ce ‘yan bindigan sun samu wani shugaba wanda yake rike da daliban makarantar da su ka rage bayan an ceto wasu a baya.

'Yan bindiga sun kawo bukatu

A cikin bukatun da sabon shugaban ‘yan ta’addan ya bada shi ne fito da wasu takwarorinsu ‘yan bindiga da ke hannun jami’an tsaro.

Ana tunanin ofishin mai ba shugaban kasa shawarar tsaro (ONSA) da hedikwatar tsaro da jami’an DSS suna tattaunawa da miyagun.

Kara karanta wannan

Majalisar UN tayi maganar rayuka 190 da aka kashe a Najeriya, Tinubu yana hutu a Legas

Wasu iyayen yaran da aka zanta da su a boye sun ce sun ga faifen bidiyo a Whatsapp inda ake nuna za a yanka wasu daliban da aka sace.

Dan Rani ya canji Ali Kachalla

Yaran Ali Kachalla wanda sojojin sama su ka kashe ake tunanin sun fito da wannan bidiyo, ana tunani Dan Rani aka zaba ya gaji kujerarsa.

Wani ‘danuwan marigayi Kachalla mai suna Ibrahim yana cikin wadanda ‘yan bindigan su ke so a fito da su daga hannun jami’an tsaro.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnati

A makon nan wani jami'in majalisar dinkin duniya yayi kira ga hukumomin Najeriya su binciki kashe-kashen rayukan da aka yi

Volker Turk ya yi tir da jeringiyar hare-haren ‘yan bindiga a kauyukan jihar Filato wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane kusan 200.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng