Ali Kachalla: Waye Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF?

Ali Kachalla: Waye Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF?

  • Ali Kachalla shine shu'umin shugaban 'yan bindigan dake dajin Kuyambana a Zamfara
  • Hatsabibin dan ta'addan shi ake zargi da harbo jirgin rundunar sojin sama a Dansadau
  • Matashin mai shekaru talatin a duniya yana da yara sama da dari biyu dake ta'addanci a kasansa

Hatsabibin shugaban masu garkuwa da mutane dake tafka tsiya a yankin Dansadau a dajin Kuyambana, Ali Kachalla, shine ke da alhakin harbo jirgin rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF), Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da aka rikito da jirgin kasa bayan amfani da bindigar baro jirgi a ranar 18 ga watan Yuni, har yanzu babu cikakken bayani kan yadda al'amarin ya faru.

KU KARANTA: Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

Ali Kachalla: Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF
Ali Kachalla: Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

Ana alakanta harbo jirgin NAF da Kachalla

Yayin da aka dinga alakanta lamarin da 'yan bindiga, an dinga zargin 'yan bindigan dake tafka tsiya a jihohin Zamfara, Neja, Kaduna, Katsina, Sokoto da Kebbi.

Kara karanta wannan

Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

Amma kuma kamar yadda mazauna yankin, jami'an tsaro da kuma masu sani a fannin suka sanar da Daily Trust, Ali Kachalla ne babban dan ta'addan dake da yara a dajin Kuyambana kuma yana da hannu a wannan aika-aikar.

Kachalla sarauta ce da kabilar Kanuri kuma shine shu'umin dan ta'addan dake aika-aika a yankin arewa maso yamma.

Yaran Kachalla ne suka harbi jirgin saman NAF kusa da kauyen Kabaru wanda ke da nisan kilomita 15 daga yammacin Dansadau.

A wata takarda da mai magana da yawun NAF Edward Gabkwet ya fitar a lokacin, ya ce an kaiwa jirgin farmaki ne yayin da ya fita aiki a iyakokin jihohin Zamfara da Kaduna.

Yayin da ba a ji komai ko ganin ragowar jirgin yakin, rundunar sojin kasa sun fitar da hotunan matukin jirgin, Flight Lieutenant Abayomi Dairo wanda cike da nasara ya samu ya fita daga jirgin.

Kara karanta wannan

Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci a Zamfara

Daga baya Daily Trust ta ruwaito yadda Dairo ya tsere inda wasu 'yan kauye suka boye shi kafin duhu yayi a kai shi Dansadau ya kwana.

Harbo jirgin saman yana daga cikin ayyukan Kachalla duk da mazauna yankin Dansadau suna ta kiran sunan Kachalla kan yadda kwanakin nan ya tsananta kai farmaki.

Waye Kachalla?

Ali Kachalla matashin dan bindiga inda yake da yara sama da 200 a dajin Kuyambana. Shi ke shugabantar dajin Zamfara, Kebbi, Kaduna da Neja.

Wadanda suka san shi sun ce an haife shi a Masada, wani karamin yanki a Dansadau. An gano cewa yana cikin shekarunsa na 30.

A ina Kachalla yake da zama a halin yanzu?

A halin yanzu Kachalla yana zama a wurin wani tafki mai suna Goron Dutse wanda ke da Nisan kilomita 25 daga kudancin garin Dansadau, wata majiya wacce take wurin ta tabbatarwa da Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

Kogin Goron Dutse yana tsakanin iyakokin jihohin Kaduna da Zamfara inda wani sashin shi yake jihar Kaduna, wani kuma Zamfara.

Wurin da yake rayuwa yana da bukkoki a kusa da Birnin Gwari. Amma da yawa daga cikin shanunsa suna nan a Zamfara," wata majiya da ta bukaci a boye sunanta ta sanar.
A yanzu da nake magana, za a iya samun yaran shi a Dandalla, Madada da Gobirawa. Kauyukan dukkansu suna kudu maso gabas dake garin Dansadau. Dukkan yankunan na karkashin 'yan bindiga," majiyar tace.

Ana kwatanta yaran Kachalla da marasa tsoro kuma sun kasance masu kai farmaki kan jami'an tsaro. An gano cewa yaransa sun fi na kowacce kungiyar 'yan ta'adda yawa.

'Yan bindiga sun kai farmaki asibitin Zamfara

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin arziki a Amurka ya kwatanta Shugaban Najeriya a zaman mai kasala

Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng