Abdussamad Rabiu Ya Hadu da Tinubu, Ya Fadi Abin da Zai Faru da Farashin Simintin BUA

Abdussamad Rabiu Ya Hadu da Tinubu, Ya Fadi Abin da Zai Faru da Farashin Simintin BUA

  • Abdul-Samad Rabiu ya kai wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ziyara ta musamman a gidan gwamnati a Legas
  • Shugaban kamfanin na BUA ya jaddada niyyarsu na ganin an cigaba da bada sarin simintinsu a kan N3, 500 a 2024
  • Alhaji Rabiu ya ce nisan da ke tsakanin garuruwa ya jawo ake ganin farashin simintin BUA ya canza da kudin sari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Alhaji Abdul-Samad Rabiu wanda shi ne shugaban kamfanin BUA Group a duniya, ya ziyarci Mai girma Bola Ahmed Tinubu.

Abdul-Samad Rabiu ya kai ziyara wajen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne a garin Legas, Daily Trust ta kawo rahoton a jiya.

BUA Group
Shugaban kamfanin simintin BUA, Abdussamad Rabiu Hoto: BUA Group
Asali: UGC

A yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a yammacin Alhamis, Abdul-Samad Rabiu, ya yi alkawarin saida buhun simintinsa kan N3, 500.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya yi hasashen tsige na hannun damar Tinubu, Gbajabiamila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin simintin BUA zai canza a 2024?

‘Dan kasuwan ya ce za su tabbatar da wannan farashi ne daga watan Junairun 2024 a yunkurinsu na ganin sun saukakawa al'umma.

Rabiu ya ce kamfaninsu zai yi bakin kokarinsa wajen ganin abokan huldarsa sun samu siminti cikin sauki, abin da yake wahala a yau.

Kalubalen da simintin BUA yake fuskanta

Attajirin ya tabbatar da ana samun kalubale wajen isar kayan kamfanin ga jama’a. Dillalai sun ce suna kashe kudi wajen jigilar simintin.

Nairametrics ta rahoto ‘dan kasuwan yana bayanin kalubalen da ake samu, amma ya ce za su fadada ta hanyar bue sabon wuri a Sokoto.

"Kun san farashin da mu ka yanke shi ne N3, 500 a kan kowane buhu. Kun san akwai farashin kamfani, sai VAT da kudin kai kaya.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya ya lissafo jihohin da talauci, wahala da rashin tsaro za su karu a 2024

Kamar yadda ku ka sani, kamfanonin da mu ke da su; daya yana Edo, daya yana Sokoto.
A dalilin haka idan ka na so mu kawo maka siminti daga Sokoto misali zuwa Legas, ko Adamawa zuwa Maiduguri, nisan akwai yawa.
Saboda haka ya danganta ne da nisan wuri. Kun san farashi yana canzawa, amma mun yi niyyar rike alkawarin da mu ka dauka.

Alhahi Abdul-Samad Rabiu

Sabanin BUA v Dangote

Tun kwanakin baya aka ji labari manyan Arewa za su yi sulhu tsakanin Alhaji Aliko Dangote da kuma Alhaji Abdussamad Isiyaku Rabiu.

Shugaban kungiyar nan ta NEF, Farfesa Ango Abdullahi ya nuna babu dalilin da attajiran za su rika rigima a fili a kan harkar kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng