Rudani Yayin Da ’Yar Shekara 4 Ta Auri Dattijo Mai Shekaru 54, Ta Fadi Dalilai Masu Tayar da Hankali
- Hankalin mutane ya tashi bayan yarinya ‘yar shekara 4 ta auri dattijo mai shekaru 54 a jihar Bayelsa
- Lamarin ya faru a kauyen Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama a jihar a ranar 26 ga watan Disamba
- Dattijon mai suna Akpos ya auri yarinyar a kauyen inda masu rajin kare hakkin kananan yara suka yi Allah wadai da auren
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa – Al’ummar kauyen Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa sun shiga rudani bayan aurar da wata yarinya ‘yar shekara 4 ga wani dattijo.
Iyayen yarinyar ne suka ba da auren yarinyar wacce ba a bayyana sunanta ba ga dattijo dan shekara 54 wanda hakan ya jawo cece-kuce a yankin.
Jimami yayin da babban mai sarautar gargajiya ya rasu ya na da shekaru 61 a duniya, bayanai sun fito
Yaushe aka daura auren yarinyar?
Dattijon mai suna Akpos ya auri yarinyar a ranar 26 ga watan Disamba inda masu rajin kare hakkin kananan yara suka yi Allah wadai da auren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta bayyana auren a matsayin babban laifi da kuma cin zarafi inda ta ce hakan ya sabawa kndin tsarin mulki, cewar Tribune.
Iyayen yarinyar sun tabbatar da cewa dattijon shi ne mijin yarinyar tun a baya kafin rayuwa inda aka kwatanta wannar al’ada da abin takaici.
Wata majiya a kauyen ta bayyana cewa yarinyar ta ce dattijon shi ne mijinta tun a rayuwarsu ta farko wanda ya mutu shekaru aru-aru.
Yarinyar ta kara da cewa ta yi ta yawo wurare daban-daban don neman mijinta amma ba ta same shi ba.
Martani kungiya kan auren
Majiyar ta ce:
“Yarinyar ta ce idan har ba a barta ta auri mijin ba, ba ta da wani abin yi a kauyen Akeddei inda ta ce za ta mutu cikin aminci.
“Don gudun kada a rasa yarinyar, iyalan sun yanke shawarar bayar da yarinyar da yin kasaitaccen biki don kara hada masoyan da suka dade da juna.”
Shugaban Gidauniyar DO reshen jihar Bayelsa, Elvis Mannie ya tabbatar da faruwar lamarin, cewar Newstral.
Mannie ya ce Gidauniyar ta fara binciken lamarin don tabbatar da ceto yarinyar daga wannan iftila’i da ta shiga.
'Yan daba sun watsa masu zabe a Bayelsa
A wani labarin, wasu 'yan daba sun watsa jama'a masu zabe a jihar Bayelsa da ke Kudancin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a yankin Agorogbene inda suka lalata akwatunan zaben tare da ji wa mutane ciwo.
Asali: Legit.ng