Gwamnatin Jihar Arewa Ta Dauki Wani Muhimmin Mataki Domin Kawo Karshen Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Arewa Ta Dauki Wani Muhimmin Mataki Domin Kawo Karshen Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Zamfara na cigaba da ƙoƙarin ganin ta kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi jihar
  • Gwamnatin ta ɗauki matakin kulle wasu kasuwannin shanu 11 a faɗin jihar saboda dalilin tsaro
  • A cewar gwamnatin ta gano ƴan bindiga na yin amfani da kasuwannin domin sayar da shanun da suka sato

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sake rufe kasuwannin shanu 11 a wasu sassan jihar har sai baba ta gani.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Munnir Haidara, ya ce an rufe kasuwannin ne sakamakon rahotannin tsaro cewa ƴan bindiga na amfani da kasuwannin wajen sayar da shanun sata, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaba Tinubu ya dira a jihar arewa bayan kashe bayin Allah sama da 100

Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin shanu 11
Gwamnatin jihar Zamfara ta kulle kasuwannin shanu 11 Hoto: @MFaarees
Asali: Twitter

Kasuwannin da abin ya shafa a cewar Haidara, su ne kasuwannin Tsafe da Bilbis da ke ƙaramar hukumar Tsafe, kasuwar Jangebe dake ƙaramar hukumar Talata-Mafara da kasuwar Wuya dake ƙaramar hukumar Anka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune kasuwar Magamin Diddi da ke ƙaramar hukumar Maradun, kasuwar Galadi a ƙaramar hukumar Shinkafi, kasuwar Mada a ƙaramar hukumar Gusau, da kasuwar Sabon Birnin Dan Ali dake ƙaramar hukumar Birnin Magaji.

Sauran kasuwannin sune Kokiya, Chigama da Nasarawar Godel duk a ƙaramar hukumar Birnin Magaji.

Meyasa gwamnatin ta rufe kasuwannin?

Kwamishinan ya bayyana cewa:

"Gwamnatin jihar ta ga ya zama dole ta rufe waɗannan kasuwanni saboda rahotannin tsaro da ke cewa ƴan bindiga na yin amfani da waɗannan kasuwanni ne domin sayar da shanun sata."

Ya ce gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda tare da cafke duk wanda ya karya dokar, rahoton TVC News ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Kotun koli: Sabuwar zanga-zanga ta barke kan shari'ar gwamnan APC da dan takarar PDP

"Tuni aka umarci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu a wadannan kasuwannin da abin ya shafa." A cewarsa.

Haidara ya yi kira ga al’ummar jihar da su bi wannan umarni tare da ba gwamnatin jihar haɗin kai a ƙoƙarinta na kawar da ƴan bindiga a jihar.

Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Kasuwanni

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe wasu kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi biyar na jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta garƙame waɗannan kasuwannin ne saboda dalilin da suka danganci matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng