Bankin Duniya Ya Lissafo Jihohin Da Talauci, Wahala da Rashin Tsaro Za Su Karu a 2024
- Matsalar rashin tsaro da wahalar halin rayuwa za ta ta’azzara sosai a shekarar 2024 da za a shiga
- Kamar yadda bincike ya nuna, matsin lambar za ta fi shafar jihohin da ke yankin Arewacin Najeriya ne
- Ana tunanin garuruwan da ke jihohin Adamawa, Borno, Kaduna, Katsina, Sokoto za su fi shiga takura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bankin duniya ya ce rayuwa za ta kara tsanani kuma akwai yiwuwar kashe-kashe su yawaita musamman a wasu jihohin Arewa.
Punch ta rahoto babban bankin na duniya yana cewa za ayi ta fama da wadannan matsaloli har zuwa watan Mayu na shekarar 2024.
Jihohin da talauci zai yi kamari
Jihohin da abin zai shafa sosai sun hada da Borno, Kaduna, Katsina, Sokoto sai kuma Zamfara da wasu bangarori a Adamawa.
Farashin mai zai zube gaba daya, malamin addini ya yi hasashen shekarar 2024, ya fadi sauran abubuwa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton da bankin ya fito ya nuna ana fuskantar matsala wajen noma a kasar, hakan zai yi tasiri wajen amfanin gona da za a samu.
Karancin kayan abinci a Afrika
Adadin kayan amfanin da za a samu a kakar 2023/2024 zai ragu da 2% idan aka kamanta da albarkar noman shekarun baya.
Matsalolin da aka samu a Najeriya za su taimaka wajen raguwar kayan abinci a nahiyar Afrika kamar yadda aka fitar a rahoto.
Sauran kasashen da za a wahala su ne: Burkina Faso, Kamaru, Chad, Mali, da Nijar.
Abinci sun yi tsada a kasuwa
Daga Nuwamba zuwa watan Mayun 2024, matsalar karancin abinci za ta fi kamari a Afrika saboda rashin tsaro da tsadar rayuwa.
Bankin duniyan ya ce daga Agusta zuwa Nuwamba, mutane da-dama suna wahala da tsadar rayuwa a sakamakon hauhawan farashi.
Masana sun hango matsala a 2024
Masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa tsadar kayan abinci a 2023 somin-tabi ne kan abin da za a gani a 2024 a jihohin Najeriya.
Dr. Abubakar Sani Abdullahi ya ce gaskiya abinci zai yi tsada a badi saboda cire tallafin fetur da rashin tsaro ya jawo an rage noma.
Kwararren ya ce irinsu wake ba su yi kyau a shekarar bana ba, kuma nan da farkon 2024 za a fara shigowa sayen kayan da aka noma.
Kasafin kudin jihohi a shekarar 2024
Kuna da labari abin da Legas za ta kashe a shekarar 2024 ya fi karfin lissafin jihohin Adamawa, Taraba, Gombe, Bauchi, Borno da Yobe.
Jihohin Ekiti, Ebonyi, Nasarawa da Gombe za su kashe N750bn, kusan daidai da kasafin da gwamnatin jihar Ribas tayi domin 2024.
Asali: Legit.ng