Kasafin Kudi: Biliyoyin da Kowane Gwamna Yake Niyyar Kashewa a Shekarar 2024
- Gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi sun kammala aiki a kan kudin da za su kashe a shekara mai zuwa
- Kasafin kudin ya kai gaban ‘yan majalisar tarayya da na dokoki a jihohi, a wasu wurare har an amince da su
- Akwai Gwamnonin da sun sa hannu a kundin kasafin 2024, an san abin da jihohinsu za su batar a badi
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Rahoton nan ya tattaro bayanan kudin da ake sa ran shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni za su kashe a 2024.
A shekarar da za a shiga gwamnatin tarayya tayi kasafin N27.50tr wanda akwai yiwuwar ‘yan majalisar tarayya su kara kudin.
Kasafin kudin kowane yanki a 2024
Idan aka koma ga jihohi, gwamnonin Kudu maso yamma za su kashe N4.2tr, na Kudu maso kudu sun yi kasafin N3.43tr a badi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin da ke jihohin Arewa maso yamma za su kashe N2.5tr, sai na Kudu maso gabas za su batar da N2.29tr a shekarar 2024.
Kasafin kudin jihohin Arewa ta tsakiya shi ne N1.89tr sai a kashe N1.60tr a Arewa maso gabas wanda shi ne mafi karanci.
Yadda jihohi za su batar da kudi
StatiSense ta tattaro kasafin kudin jihohi 36 da ake da su kuma za a fahimci Legas ce a kan gaba da ta ke shirin kashe tiriliyoyi.
Daga Kudu akwai Akwa Ibom, Ogun, Delta, Imo, Ribas, Bayelsa da Enugu su na cikin jihohi masu kasafin kudi mai yawa a 2024.
Ba a bar irinsu Neja a baya ba wanda gwamna Umar Bango ya gabatar da kasafin N613bn sai Kaduna, Katsina, Kano da Zamfara.
Nawa gwamnoni za su kashe?
1. Abia: ₦567.20bn
2. Adamawa: ₦225.89bn
3. Akwa Ibom: ₦845.63bn
4. Anambra: ₦410.10bn
5. Bauchi: ₦300.22bn
6. Bayelsa: ₦480.99bn
7. Benuwai: ₦225.73bn
8. Borno: ₦340.62bn
9. Kuros Riba: ₦250bn
10. Delta: ₦724.90bn
11. Ebonyi: ₦202.13bn
12. Edo: ₦325.30bn
13. Ekiti: ₦159.57bn
14. Enugu: ₦521.56bn
15. Gombe: ₦207.75bn
16. Imo: ₦592.23bn 17
17. Jigawa: ₦298.14bn
18. Kaduna: ₦458.27bn
19. Kano: ₦350.20bn
20. Katsina: ₦454.31bn
21. Kebbi: ₦250.13bn
22. Kogi: ₦258.28bn
23. Kwara: ₦286.40bn
24. Legas: ₦2.25tn
25. Nasarawa: ₦199.88bn
26. Neja: ₦613.27bb
27. Ogun: ₦703.03bn
28. Ondo: ₦384.53bn
29. Osun: ₦273.91bn
30. Oyo: ₦434.22bn
31. Filato: ₦295.43bn
32. Ribas: ₦800.39bn
33. Sokoto: ₦270.10bn
34. Taraba: ₦311.39bn
35. Yobe: ₦217.00bn
36. Zamfara: ₦423.52bn
Kasafin kudin Bola Tinubu a 2024
Ana da labari Majalisar tarayya tana fatan a kammala zama a kan kundin kasafin kudin 2024 kafin karshen shekarar bana
Sanata Opeyemi Micheal Bamidele ya ce ‘yan majalisa da Sanatoci sun kusa gama aiki, a amince da kasafin kudin na 2024.
Asali: Legit.ng