Abin Da Shugaba Tinubu Ya Fadawa Gwamnonin Najeriya a Legas

Abin Da Shugaba Tinubu Ya Fadawa Gwamnonin Najeriya a Legas

  • Shugaba Tinubu ya ce a shirye yake ya hada kai da gwamnonin Najeriya domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar
  • Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Talata, 26 ga watan Disamba a lokacin da ya gana da gwamnonin Najeriya a gidansa da ke Legas
  • Shugaban ya kuma yabawa Gwamna Fubara a wajen taron bisa kokarin da yake yi na warware matsalolin siyasar jihar Rivers cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata, 26 ga watan Disamba, ya ce dole ne gwamnatocin tarayya da na jihohi su kasance masu daukar alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kara karanta wannan

Za mu shawo kan dukkan matsaloli tare da karfafa Najeriya - Ganduje

Tinubu ya jaddada bukatar samar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da tarayya domin samar da ci gaban ababen more rayuwa cikin gaggawa a fadin kasar nan.

Tinubu ya gana da gwamnonin Najeriya a Legas
Abin da shugaba Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya a Legas. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Abin da Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya

Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya a gidansa da ke Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce:

“Ina so mu yi watsi da rabe-raben titunan tarayya, jiha ko karkara.
"Dole ne mu yarda cewa kawo ci gaba hakki ne da ya rataya a wuyanmu baki daya, mu ba da fifiko ga 'ya'yanmu.
"Dole ne shirin ciyar da dalibai abinci ya dawo cikin gaggawa, tun daga kananan hukumomi zuwa gwamnatocin jihohi da na tarayya."

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a shafin X (tsohuwar Twitter) @NGRPresident.

Kara karanta wannan

Akwai haske a 2024: Tinubu ya yi gagarumin alkawari gabannin shiga sabuwar shekara, ya fadi dalili

Gwamnonin Najeriya sun gana da Shugaba Tinubu a Legas

Biyo bayan ganawarsu a fadar gwamnatin jihar Legas da ke Marina, mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya sun gana da Shugaba Tinubu a gidan sa da ke Legas.

Babban mai tallafawa gwamna Sanwo-Olu kan kafofin watsa labarai, Jubril Gawat ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Talata, Legit Hausa ta ruwaito.

Ya rubuta cewa:

"Kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin shugabancin @RealAARahman sun taru a Legas, fadar gwamnatin jihar da ke Marina. Daga nan suka zarce gidan shugaban kasa a Legas.
"Zababben gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo na daga cikin tawagar gwamnonin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.