Gwamnan Najeriya Ya Mutu Yana Jinya a Asibitin Kasar Waje
- Ajali ya kira Mai girma Gwamnan Ondo watau Rotimi Akeredolu awanni bayan bikin kirismeti a duniya
- Gwamnan na jihar Ondo ya yi wata da watanni a kan gadon asibiti, yana ta jinya a gida da kasashen waje
- Wasu sun ce Akeredolu ya mutu ne a hannun likitoci a Legas bayan nada gwamnan rikon kwarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya rasu a sakamakon wasu rashin lafiya da ya dade yana jinya a kai.
The Nation ta ce Mai girma Rotimi Akeredolu ya bar duniya ne yana mai shekara 67.
A ina Rotimi Akeredolu ya mutu?
Rahoton Vanguard ya ce Marigayin ya mutu ne a hannun likitocin gwamnati da ke Legas a safiyar ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiya ta shaida cewa na-kusa da Akeredolu sun gagara fitar da shi zuwa asibitocin kasar waje inda yake ta jinya.
Wasu rahotannin sun ce ‘dan siyasar ya cika ne yayin da ake kokarin kai kayan aiki domin duba shi a garin Legas.
“Akeredolu ya mutu; ya rasu ne a Legas
Suna ta neman injin wankin koda ne da za a kawo zuwa inda yake a boye.”
- Majiya
Ko da labarin ya zo a jaridar Sahara Reporters, babu wata sanarwa a hukumance da ta fito daga gwamnati.
...Akeredolu ya mutu ne Jamus
Rahoton Premium Times ya sha bam-bam inda ya nuna gwamnan ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Jamis.
Wata majiyar ta ce da kimanin karfe 2:00 na dare ne tsohon shugaban kungiyar lauyoyin kasar ya cika.
Akeredolu ya yi ta fama da cutar dajin jini da na mahaifa wanda ya sa Lucky Ayedatiwa ya karbi mulki.
Rashin lafiyar Rotimi Akeredolu
Tun tuni gwamnan ya kwanta rashin lafiya, abin da ya yi sanadiyyar fita da shi zuwa kasar waje kwanakin baya.
Da aka shafe kwanaki bai dawo ba, gwamnan ya tsawaita wa’adin hutun da ya dauka a majalisar dokokin Ondo.
Sai daga baya Rotimi Akeredolu ya dawo Najeriya, duk da haka bai shiga ofis ba, ana zargin ya zauna ne a Ibadan.
Rasuwar Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba
A yau aka samu labari Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba ya rasu a makon nan yana mai shekara 68 da haihuwa.
Marigayi Ghali Umar Na’Abba ya yi tashe ne a lokacin da Olusegun Obasanjo yake mulki tsakanin 1990 da 2003.
Asali: Legit.ng