Salman Rushdie Da Yayi Batanci Ga Annabi Ya Rasa Ido Daya Kuma Hannu Daya Ya Shanye

Salman Rushdie Da Yayi Batanci Ga Annabi Ya Rasa Ido Daya Kuma Hannu Daya Ya Shanye

  • Salman Rushdie, marubucin da ya yi batanci ga Annabi Muhammadu SAW ya rasa ido da hannu daya
  • Hakan ya biyo bayan da'ba masa wuka da wani matashi yayi a birnin New York dake Amruka
  • Gwamnatin Iran ta ba da sanarwar ba da lada mai yawa ga wanda ya kashe Rushdie tun bayan wani rubutu da ya yi

Shahrarren marubuci wanda yayi kalaman batanci ga Annabi (SAW), Salman Rushdie, ya rasa ido daya kuma hannunsa daya ya shanye sakamakon harin da wani matashi ya kai masa.

Wakilinsa, Andrew Wylie, ya tabbatar da hakan a hirar da yayi da El Pais dake kasar Andalus.

Watanni biyu kenan da suka gabata wani matashi ya farmaki Salman Rushdie a birnin New York dake Amurka bisa kalaman batancin da ya yiwa Annabi shekarun baya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa

Rushdie
Salman Rushdie Da Yayi Batanci Ga Annabi Ya Rasa Ido Daya Kuma Hannu Daya Ya Shanye
Asali: AFP

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Raunukan da ya samu na da yawa, amma ya rasa idonsa. An saresa sai uku a wuya. Hannun daya ya shanye saboda jijiyoyin hannunsa sun yanke."
"Kuma ya samu wasu raunuka 15 a kirji da ha'ba."
"Babbar matsalar da yake fuskanta dai itace Fatawan da akayi shekarun baya wanda yasa wani matashi ya kai masa hari."

Wylie dai ya ki bayyana ainihin inda Salman Rushdie ke kwance yanzu saboda tabbatar da tsaro.

An Farmaki Fitaccen Marubuci, Salman Rushdie, Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW

A tun farko, wani mutumi ya kai wa shahararren marubucin nan, Salman Rushdie, hari yayin da yake kan dandamali zai yi jawabi a ƙasar Amurka.

Marubucin, wanda aka shafe tsawon shekaru ana masa bazaranar kisa saboda ya rubuta wani littafi, 'The Satanic Verses,' da ake zargin ya yi batanci ga Annabi SAW, an farmake shi ne a wani gari dake yammacin New York.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya

A wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa, ta ce wani mutumi ya yi fitar burgu zuwa kan dandamalin da Marubucin ke shirin gudanar da Lakca, inda ya rinka bugunsa yana daɓa masa wuka.

Bayan an dauke shi a jirgin sama zuwa asibiti inda ya shafe sa'o'i a dakin tiyata, Rushdie yana kan na'urar numfashi kuma ya kasa magana tun da yammacin Juma'a, Al-Jazeera ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel