Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Halaka Babban Likita a Yanayi Mara Dadi a Gaban Iyalansa
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun jr har cikin gida sun tafka ta'asa a garin Kanɓi da ke ƙaramar hukumar Moro ta jihar Kwara
- Miyagun ƴan bindigan waɗandan ake zargin makasan haya ne sun halaka wani babban likita a gaban iyalansa
- Ƴan bindigan bayan sun halaka likitan sun yi awon gaba da ɗiyarsa mai shekara 23 da haihuwa a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton makasa ne sun kashe wani Dokta David Adefikayo, shugaban asibitin Dafikayo a gidansa da ke Kanbi a ƙaramar hukumar Moro a jihar Kwara.
Jaridar Daily Trust ta ce maharan sun shiga gidan marigayin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Alhamis inda suka yi wa likitan kisan gilla a gaban matarsa da ƴaƴansa.
An tattaro cewa roƙon da likitan ya yi wa ƴan bindigan da su karɓi kuɗi su kyale shi ya faɗa kan kunnen uwar shegu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma ce sun yi garkuwa da ɗaya daga cikin ƴaƴan likitan da aka kashe, mai suna Christiana Adejoke Alabi, mai shekara 23.
Jaridar Channels tv ta ce ƴan bindigan sun sako ɗiyar likitan a ranar Juma'a, kwana ɗaya bayan sace ta.
Mummunan lamarin dai, kamar yadda aka tattaro, ya haifar da kaɗuwa da alhini a cikin al’umma, domin marigayin likitan mutum ne mai mutuntawa wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen kula da lafiyar al’umma.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ejire Adeyemi-Adetoun, ta tabbatar da faruwar lamarin.
A kalamanta:
"Eh, sun kashe likitan tare da sace ɗiyarsa mace ƴar shekara 23 a lokacin da lamarin ya faru."
"DPO da sauran jami'an tsaro sun kutsa cikin daji domin neman ƴan bindigan da kuma yiwuwar ceto ɗiyar likitan."
Ƴan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon mummunan hari a jihar Plateau.
Ƴan bindigan sun kai harin ne kan masu shirye-shiryen bikin Kirsimeti a ƙauyen Gana Ropp da ƙaramar hukumar Barikin Ladi, inda suka halaka mutum ɗaya da raunata mutum biyu.
Asali: Legit.ng