Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Kan Masu Shirin Bikin Addini a Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Kan Masu Shirin Bikin Addini a Jihar Arewa

  • Yan bindiga sun kai sabon hari mai muni kan mutane yayin da suke shirin zuwa kirsimeti a jihar Filato
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun halaka wani matashi ɗan shekara 19, sannan sun jikkata wasu mutum biyu
  • Rundunar Operation Save Haven ta ce dakarun soji sun yi kokarin daƙile harin tun kafin ɓarnar ta wuce haka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Wasu tsagerun ƴan bindiga sun halaka matashi ɗan shekara 19, Jude Nicodemus, tare da jikkata wasu mutum biyu a mummunan harin da suka kai a jihar Filato.

Kamar yadda jaridar The Nation da ruwaito, ƴan bindigan sun tafka wannan aika-aika ne a kauyen Gana Ropp da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi.

Kara karanta wannan

Kotun koli na shirin yanke hukunci, wasu tsageru sun yi yunƙurin ƙona gidan gwamnatin Kano

Gwamnan Filato, Celeb Mutfwang.
Yan bindiga sun kashe matashi dan shekara 19, sun jikkata wasu a Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kai wannan sabon harin ne kan masu shirye-shiryen bikin kirsimeti a daren ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin rundunar 'Operation Safe Haven’ (OPSH), Kaftin James Oya, ya tabbatar da faruwar wannan hari ga manema labarai da safiyar ranar Alhamis.

Oya ya ce:

"Eh tabbas lamarin ya faru, harin babu daɗi domin maharan sun shigo ne kwatsam suka buɗe wa masu shirye-shiryen kirsimeti wuta, nan take mutum ɗaya ya mutu."

Ya ƙara da cewa ba dan hanzarin kai ɗaukin sojoji ba da wataƙila asarar rayukan ta zarce haka, yana mai cewa mutum ɗaya ne ya rasa ransa, wasu biyu suka jikkata.

Wannan dai na ɗaya daga cikin sabbin munanan hare-hare da kisa wanda maharan suka kaddamar a yankunan Barkin Ladi, Riyom, Bokkos da kuma Mangu.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

An tattaro cewa sun sha alwashin hana jama'a gudanar da bukukuwan kirsimeti cikin kwanciyar hankali.

Matasa sun yi magana kan yawan hare-hare

Kungiyar matasan Berom (BYM) karkashin jagorancin Solomon Dalyop Mwantiri, ta yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar kwanan nan.

Kungiyar ta bukaci rundunar sojin Operation Safe Haven (OPSH) karkashin jagorancin Manjo Janar AE Abdulsallam da su kara zage damtse wajen magance matsalar ta’addanci.

Ta kuma yi kira da a gaggauta kakkaɓe ‘yan ta’adda da aka gano suna zaune a tsaunin Were a Ropp, karamar hukumar Barkin Ladi, da wasu sassa na jihar Filato.

Wani Matashin Ango Ya Mutu Kwana Uku Kafin Ɗaura Aurensa

A wani rahoton kuma Wani Ango mai jiran gado wanda ya rage saura kwanaki uku a ɗaura masa aure, Abraham Basif, ya riga mu gidan gaskiya.

Abokan angon sun shiga jimami da kaɗuwa yayin da suka samu labarin rasuwar awanni 72 kaɗai gabanin a ɗaura masa aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel