Shehu Sani Ya Yi Magana Mai Muhimmanci Bayan Matatar Mai Ta Port Harcourt Ta Fara Aiki
- Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana fatan cewa matatar mai ta Kaduna za ta fara aiki nan ba da jimawa ba
- Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan rahotannin cewa matatar mai ta Port Harcourt ta fara aiki
- Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya cika alƙawarin da ya yi na wa’adin watan Disamba na matatar man za ta fara aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Port Harcourt, jihar Rivers - Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, ya yabawa gwamnatin Bola Tinubu kan fara aikin matatar mai ta Port Harcourt.
Matatar man ta birnin Port Harcourt ta fara aiki ne bayan an ɗauki lokaci mai tsawo ana aikin gyara.
A sake farfado da matatar mai ta Kaduna - Sani
Bayan matatun man fetur ɗin sun daina aiki a shekarar 2019, matatun mai guda uku da ake da su a ƙasar nan na Port Harcourt, Warri, da Kaduna na da ƙarfin tace ganga 445,000 a kowace rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da haka, matatun sun zama marasa aiki saboda matsalolin kula da su.
Da yake mayar da martani game da wannan cigaban, Sani ya bayyana fatansa na cewa matatar mai ta Kaduna ita ma za ta dawo aiki.
Shehu Sani a wani saƙo da ya rubuta a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), ya bayyana cewa:
"Fara aikin matatar mai ta Port Harcourt abin yabawa ne. Hukumar NNPC ta cika alkawarin da ta ɗauka na cika wa'adin Disamba. Godiya ga GCEO, ma'aikata, da FG."
"Muna fatan matatar mai ta Kaduna da ta kwashe fiye da shekara 10 ba ta aiki za ta dawo aiki nan bada jimawa ba."
Matatar Man Dangote Ta Fara Aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man fetur ta Dangote ta fara aiki bayan an kwashe tsawon lokaci ana jiran zuwan ranar fara aikinta.
Matatar mai ta Dangote ya sanar da fara karɓar ganga miliyan ɗaya ta ɗanyen man fetur daga kamfanin hada-hadar mai ta duniya mai suna Shell (STASCO).
Asali: Legit.ng