Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya
- Ministar ta ce a halin yanzu fiye da yara miliyan 9 ke cin gajiyar abinci mai gina jiki sau daya a rana a fadin kasar
- Sannan za a kara adadin daliban zuwa miliyan 14 nan da shekarar 2023
- Gwamnatin Jihar Neja ta bukaci ma’aikatar da ta fadada ciyarwar zuwa sauran daliban aji 4-6
Gwamnatin Tarayya za ta kara adadin daliban makarantun firamare da take ciyar wa daga miliyan tara zuwa miliyan 14 a karkashin shirinta na Ciyar da Daliban Makarantu na Kasa (NHGSFP).
Ministar Jin kai da Agaji, Hajiya Sadiya Farouk, ce ta bayyana hakan a lokacin da ta jagoranci wani ayari inda suka ziyarci Sakataren Gwamnatin Jihar Neja Ahmed Matane a ranar Juma’ah, rahoton Ptimes.
Ministar wacce mataimakin darakta a ma’aikatar Hezekiah Sunday, ta ce ayarin ya ziyarci jihar ce domin nazarin masu cin gajiyar shirin tare da duba yadda za a fadada shi.
Ta ce a halin yanzu fiye da yara miliyan tara ne ke amfana da shirin ciyar da dalibai lafiyayyen abinci sau daya a rana a duk fadin kasar nan sannan an bukaci ma’aikatar da ta kara dalibai miliyan biyar zuwa shekarar 2023, riwayar NairaMetrics.
Ta kara da cewa a karkashin shirin an dauki masu dafa abinci fiye da 100,000 sannan kananan manoma fiye da 100,000 na amfana daga shirin.
DUBA NAN: Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa
KU KARANTA: Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki
Da yake mayar da jawabi, Mista Matane ya bayar da tabbacin cewa jihar za ta ci gaba da bada hadin kan da ya dace domin ganin shirin ya yi nasara.
Ya jinjina wa kokarin ma’aikatar kan ci gaba da kawance da goyon bayan da take bai wa jihar ta hanyar samar wa da masu gudun hijira da wadanda ambaliya ta shafa kayayyakin tallafi.
Sannan ya yi kira ga ma’aikatar da ta fadada shirin ciyarwar zuwa daliban aji hudu har shida da zimmar karfafa gwiwar yaran suna zuwa sannan su zauna a makaranta.
“Ciyar da wadansu daliban sannan a ki ciyar da wadansu zai haifar da matsala tsakaninsu. Ya kamata a sauya fasalin shirin ta yadda kowane dalibi zai samu abinci,”
inji shi.
DSS ta kama malamai, jami'ai da masu sayar da abinci kan karkatar da kayayyaki
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kame malamai da jami'an yanki da ke kula da shirin ciyar da daliban makarantu na gwamnatin tarayya bisa zargin yin zagon kasa ga shirin.
An kuma kama wasu masu sayar da abinci guda 10 da ake zargi da hada baki da malamai da kuma ma’aikatan yankin don sauya tsarin, jaridar Thisday ta ruwaito.
Asali: Legit.ng