Bikin Kirsimeti: Yan Sanda Sun Gano Bindigu An Boye Su Cikin Buhu a Wata Jihar Kudu
- Biyo bayan samun ingantaccen rahoto, rundunar 'yan sanda ta samu nasar gano wasu makamai da aka boye su a cikin wani buhu a jihar Delta
- Wannan nasarar a cewar rundunar na daga cikin tsarin da kwamishinan 'yan sandan jihar, Mr Wale Abass ya kawo na dakile harin 'yan ta'adda
- Sai dai har yanzu rundunar ba ta samu nasarar kama ko da mutum daya daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu a ajiye makaman ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Delta - Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta ce ta gano makamai da harsasai a wani garin Ekpan da ke karamar hukumar Uvwie da ke jihar.
Mai magana da yawun runduar, DSP Bright Edafe, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a garin Warri.
Edafe ya ce babban shugaban ofishin 'yan sanda na lardin Ekpan, CSP Aliyu Shaba, ya samu rahotannin sirri kan yunkurin tada kayar baya a Ekpan, Warri da makwaftansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce DPO Shaba ya jagoranci tawagar jami'an ofishinsa inda suka bi diddigin wadanda ake zargi da son aikata miyagun ayyukan, The Punch ta ruwaito.
Makaman da aka kwato da kokarin 'yan sanda
A cewarsa:
"DPO din ya samu nasarar bin diddigin bata garin har zuwa mabuyarsu a bayan NIGER-CAT, sai dai ganin 'yan sandan ya sa suka tsere, ba tare da wata nasara ta kama ko da mutum daya ba.
"A yayin binciken mabuyar, an gano bindigogi da harasai cikin wani buhu, da suka hada da bindiga kirar AR, harsasai mau carbi guda biyu, harsasai mau tsayin 7.62mm guda 75.
Ya kara da cewa:
"An kuma gano bindiga kirar baushe, da bindiga 'yar Awka da dogon harashi mai tsayin 9mm. Har yanzu ana ci gaba da bincike don gano bata garin."
DSP Bright Edafe ya yi nuni da cewa tsarin da kwamishinan 'yan sanda na jihar Mr Wale Abass ya yi amfani da su na aiki wajen dakile harin ta'addanci yayin bukukuwan Kirsimeti.
Saurayi ya kashe budurwarsa kan naira dubu 5
A wani labarin, wani matashi mai shekara 19 Muhammad Ibrahim ya kashe budurwarsa saboda ta nemi ya biya naira dubu biyar bayan ta biya masa bukatarsa.
Hatsaniya kan biyan kudin ta kaure tsakanin masoyan har ta kai ga doki in doke ka, abin ya zo da karar kwana Ibrahim ya daba wa budurwar wuka.
Asali: Legit.ng