'Yan sanda sun gano miyagun makamai masu dimbin yawa a wata jihar Arewa

'Yan sanda sun gano miyagun makamai masu dimbin yawa a wata jihar Arewa

- Hukumar yan sanda ta jahar Kebbi ta sami bindigogi 30 da wasu miyagun makamai 650

- A watan daya gabata ne hukumar ta bada umarnin duk wanda yake da bindiga a jahar ya mayar wa mai ita

- Kwamishinan yan sanda yace sun sami bindigogi kirar Ak47 guda 13

Hukumar yan sanda ta jahar Kebbi ta kama bindigogi 30 da wasu makamai 650 a kokarin kare jahar daga muyagun ayyuka.

Kwamishinan yan sanda, Ibrahim Kabiru, yace sun sami bindigogi 13 kirar AK47, kirar pistol guda daya, guda shida mai baki biyu, guda takwas mai baki daya, da wasu makaman guda 650 wanda ya hada da harsashi guda 32.

'Yan sanda sun gano miyagun makamai masu dimbin yawa a wata jihar Arewa
'Yan sanda sun gano miyagun makamai masu dimbin yawa a wata jihar Arewa

KU KARANTA: An kuma: Makiyaya sun kara kai hari Coci a jihar Benuwe, sun kashe mutane bakwai

Yace an kama makaman ne a yayin da suke kokarin karbe kore wanzuwar makamai ba bisa ka'idar da Sufeta Janar na hukumar ya bayar

A watan daya gabata ne jahar ta bayar da wa'adin kwanaki 30 ga duk wani da yake da bindiga daya maidawa hukumar yan sanda ta koya fuskanci hukunci daga yan sanda.

Kwamishinan a lokacin da yake bayyanawa manema labarai yace sunanan kan bakansu na kawo karshen ta'addanci a jahar ta Kebbi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164