Innalillahi: Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 30, an Tafka Asarar Fiye da Miliyan 300 Sanadinta

Innalillahi: Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 30, an Tafka Asarar Fiye da Miliyan 300 Sanadinta

  • ‘Yan kasuwa sun shiga wani irin yanayi bayan mummunar gobara ta lakume shaguna fiye da 30 a jihar Anambra
  • Lamarin ya faru a yau Laraba 20 ga watan Disamba a kasuwar Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa
  • Shugaban kasuwar, Chif Paul Okafor ya bayyana cewa gobarar ta fara ne daga wani shago kafin ta yadu zuwa sauran shagunan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra – Mummunan gobara ta lakume shaguna akalla 30 a babbar kasuwar Nkpor da ke jihar Anambra.

Lamarin ya faru a yau Laraba 20 ga watan Disamba inda aka tafka mummunan asara a kasuwar da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yi murabus daga gwamnatin Tinubu, Lalong ya magantu

Gobara ta lakumae shaguna 30 da asarar miliyan 300
Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 30 a Jihar Anamra. Hoto: Charles Soludo.
Asali: Facebook

Shaguna nawa gobarar ta lakume?

Wakilin Punch ya tabbatar cewa gobarar ta lakume shaguna fiye da 30 kafin ‘yan kasuwar su dakile wutar kafin zuwan hukumar kashe gobara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasuwar, Chif Paul Okafor ya bayyana cewa gobarar ta fara ne daga wani shago kafin ta yadu zuwa sauran shagunan.

Okafor ya ce akalla an tafka asarar fiye da naira miliyan 300 sanadin gobarar a kasuwar, cewar Daily Post.

Shugaban kasuwar wanda shi ma shagonsa ya kone kurmus ya ce shagunan da wutar ta cinye su na makare da kaya.

Wane kira aka yi wa gwamnatin jihar?

Ya ce duk kokarin da su ka yi wurin kirar hukumar kashe gobara bai yi amfani ba saboda ba su zo wurin a kan lokaci ba.

Ya kara da cewa sai da su ka nemi mafita don kashe gobarar da kansu kafin hukumar ta samu isowa wurin, cewar NewsNow.

Kara karanta wannan

Hutun Kirsimeti: Tinubu ya zabtare rabin farashin ababen hawa, tafiya a jirgin kasa kyauta ne

Ya kira yi gwamnatin jihar ta samar da hukumar kashe gobarar kusa da kasuwar wanda zai taimaka wa kasuwanni ukun da su ke kusa da wurin.

Shugaban hukumar kashe gobara a jihar, Martin Agbili bai samu damar amsa kiran waya da manema labarai su ka masa ba.

Gobara ta lakume dukiyar miliyan 25

A wani labarin, mummunan gobara ta jawo asarar fiye da miliyan 25 a kasuwar Watt da ke jihar Cross River.

Ana zargin wayoyin wuta da ke rataye a saman kasuwar ce su ka yi sanadin gobarar da ya jawo asara marar misaltuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.